fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Tag: Bauch covi19

Gwamnan Bauchi ya kaddamar da rabon kayan Tallafin Coronavirus/COVID-19

Gwamnan Bauchi ya kaddamar da rabon kayan Tallafin Coronavirus/COVID-19

Siyasa
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad kenan a wadannan hotunan yayin da ya kaddamar da rabon kayan tallafin Coronavirus/COVID-19.   Gwamnan a sanarwar daya fitar ta shafinshi na sada zumunta ya bayyana godiya ga wadanda suka bayar da tallafi. https://twitter.com/SenBalaMohammed/status/1293208046987096066?s=19 Gwamnan ya kuma bayyana cewa, zasu bayar da tallafin ta yanda kowane mutum 1 zai samu buhun shinkafa dana Filawa da gishiri da Katan din Indomie da man girki da dai sauransu.
Jihar Bauchi ta sallami karin mutum 6 bayan sun warke daga cutar coronavirus/covid-19

Jihar Bauchi ta sallami karin mutum 6 bayan sun warke daga cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
An samu karin mutum 10 wadanda suka harbu da cutar coronavirus a jihar Bauch baya ga haka jihar ta sanar da Kara sallamar mutum 6 bayan sun warke garau daga cutar a jihar. Sai dai a rahoton da jihar ta fitar a ranar laraba ta bayyana cewa an samu karin mutuwar mutum daya wanda ya mutu a sakamakon cutar a dai dai lokacin da yake karbar kulawa a karkashin Jami'an lafiya a jihar.
Jahar Bauchi takara samun mutuwar mutum 1 mai cutar coronavirus/covid-19

Jahar Bauchi takara samun mutuwar mutum 1 mai cutar coronavirus/covid-19

Kiwon Lafiya
Jihar bauch ta sake bada rahoton mtuwar wani mai dauke da cutar coronavirus a jahar. Mara lafiyan ya mutu yayin da yake karbar magani a cibiyar keɓewar jihar. A kalla an samu rahoton mutuwar mutum 8 wanda suka mutu a sakamakon cutar. A bayanan da Ma'aikatar lafiyar jahar  ta bayar kwanan-nan ta bayyana cewa an samu karin mutum 2 masu dauke da cutar coronavirus, haka zalika an yi nasarar sallamar mutum 6 wanda suka warke daga cutar a jihar Bauchi.   Ya zuwa yanzu jahar tai nasarar sallamar adadin mutum 220 jimulla.