fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Bauch

Bayan Kashe matasa saboda zargin satar Kaza, Kotu ta dauki babban mataki akan hukumar ‘Yansanda a Bauchi

Bayan Kashe matasa saboda zargin satar Kaza, Kotu ta dauki babban mataki akan hukumar ‘Yansanda a Bauchi

Tsaro
Wata Kotun Tarayya a Bauchi ta umarci ƴan sandan Najeriya su biya diyyar naira miliyan 210 kan kashe wasu mutane biyu bayan azabtar da su da jikkata mutum guda kan zargin satar kaza. Abdulwahab Bello da Ibrahim Babangida da Ibrahim Samaila, an cafke su tare da lakada musu duka a watan Yulin shekarar da ta gabata, kan zargi satar kazar wani tsohon ɗan sanda. Azabtar da su da aka yi, ya kai ga Samaila da Babangida sun mutu, yayinda Bello ya tsira da muggan raunuka da ke barazana ga rayuwarsa. Bello ya shigar da ƙara da neman diyyar naira miliyan 150 ga kowanne daga cikinsu. Jaridar Punch ta rawaito cewa alkalin da ya yanke hukuncin ya ce laifukan da aka aikata sun take hakkinsu kamar yada ya ke ƙunshe a kudin tsarin mulkin Najeriya. Sanna ya ƙara cewa abin da ƴansanda suka aikata...
Gwamnatin Bauchi ta kaddamar da shirinta na dasa bishiyoyi don yaki da kwararowar Hamada

Gwamnatin Bauchi ta kaddamar da shirinta na dasa bishiyoyi don yaki da kwararowar Hamada

Kiwon Lafiya
A wani yunkuri na kare muhalli da kuma yaki da kwararowar hamada, gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da dashen bishiyoyi 5,000 a fadin jihar wanda aka gudanar a Sabon Kaura, wani yanki da ke cikin garin Bauchi. A yayin kaddamar da atisayen a ranar Asabar, Kwamishinan Muhalli da Gidaje, Hamisu Muazu ya bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na gwamnatin jihar domin yaki da kwararowar hamada tare da nufin magance matsaloli muhalli a jihar.    
Gwamnatin jihar Bauchi zata gudanar da rigakafin Al’lurar kyanda ga yara Dubu 400 a jihar

Gwamnatin jihar Bauchi zata gudanar da rigakafin Al’lurar kyanda ga yara Dubu 400 a jihar

Kiwon Lafiya
Akalla yara dubu dari hudu, 'yan shekaru 9 - 15, a jihar Bauchi za a yi masu allurar rigakafin cutar kyanda domin inganta garkuwar jikin su. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Gudanarwar na Hukumar Lafiya a Jihar Bauchi (BASPHCDA), Dakta Rilwanu Mohammed, yayin kaddamar da allurar rigakafin mako guda da aka saba yi a jihar ranar Litinin. Ya ci gaba da bayanin cewa hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NAPHCDA) ce ta bullo da sabon shirin wanda aka tsara da nufin taimakawa wajen bunkasa garkuwar jikin yara, yana mai kira ga iyaye mata da su tabbatar da cewa yaransu sun karbi allurar. A cewarsa, Ma'aikatan lafiya a jihar zasu karade jihar domin gudanar da wannan aikin.
Manoma 5,000 ne su kai rajista Domin shirin noman citta A Jihar Bauchi

Manoma 5,000 ne su kai rajista Domin shirin noman citta A Jihar Bauchi

Kasuwanci
Kungiyar gamayyar masu noman citta, tare da sarrafata da kasuwancinta dake jihar Bauchi, ta ce ta yi wa wasu manoma 5,000 rajista wadanda suka nuna sha’awarsu kan harkar noman citta. Alhaji Ahmed Mohammed, ko'odinetan shirin, shine ya sahida hakan ga kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a jihar Bauchi ranar Juma’a. Inda ya bayyana cewa A kalla manoma 5,000 ne su ka yi rajista a dukkan kananan hukumomi 20 na jihar. Ya kara da cewa shirin zai samar da ayyukan yi ga matasa Kimanin 20,000 A jihar.
Covid-19: Gwamnan Jihar Bauchi ya Kaddamar Da Rabon kayan tallafi ga Al’ummar Jihar

Covid-19: Gwamnan Jihar Bauchi ya Kaddamar Da Rabon kayan tallafi ga Al’ummar Jihar

Kiwon Lafiya
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya kaddamar da rabon kayan tallafi ga jama'ar jihar Bauchi dake dukkanin kananan hukumomin jihar. Gwamnan ya gabatar da rabon kayayyakin ne a ranar Talata wadanda za'a raba su ga al'ummar jihar domin rage radadi a sakamakon cutar Coronavirus. Kayayayakin da za'a raba sun hadar da Shinkafa, Masara, Wake, Taliya, Gishiri, Sukari, Mai, Gero hadi da Doya. Haka zalika gwamnan ya gargadi  cewa, gwamnatin sa bazata lamunci wani ko wasu su karkatar da kayayyakin zuwa wata hanyar ta Daban ba.