
Dan majalisar jihar Bauchi ya kamu da Coronavirus/COVID-19
Dan majalisar jihar Bauchi me wakiltar Toro/Jama'a, Honorabul Tukur Ibrahim ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.
Kakakin majalisar, Abubakar Sulaimanne ya tabbatar da haka a yau Litinin a zama na musamman da majalisar ta yi.
Yace ana kula da dan majalisar a daya daga cikin wajajan killace masu cutar dake jihar inda kuma yace an dauki samfurin wasu 'yan Majalisar inda za'a gwadasu.
Ya kuma jagoranci yiwa dan majalisar da cutar ta kama addu'ar samun sauki.