fbpx
Friday, February 26
Shadow

Tag: Bayelsa

An gano gawar ‘yansanda 6 da suka nutse a Bayelsa

An gano gawar ‘yansanda 6 da suka nutse a Bayelsa

Uncategorized
Hukumar 'yansandan Jihar Bayelsa ta sanar da Gano Gawarwakin 'yansanda 6 da suka nutse a Southern Ijaw ranar Asabar din dsta gabata yayin da suke kan hanyar zuwa wajan zaben cike Gurbi.   Kakakin 'yansandan jihar, Asinim Butswat ya bayyanawa TVC cewa an kai Gawarwakin Mutuware. “The unfortunate incident occurred on Friday, December 4, 2020, when one of the speedboats conveying eleven Policemen from Yenagoa to Southern Ijaw capsized at Oporoma. Five of the Policemen were rescued immediately, while six were missing,” according to a police statement.
Yansandan Najeriya sun nutse a Ruwa sun Mutu

Yansandan Najeriya sun nutse a Ruwa sun Mutu

Siyasa
Yansanda 3 ne suka rasa rayukansu dake kan hanyar zuwa wajan Zaben jihar Bayelsa.   Sun rasu ne a yayin da suke kan hanyar zuwa karamar hukumar South Ijaw dan gudanar da aikin zabe bayan da Jirgin ruwan da suke ciki ya nutse.   Ana zabenne dan cike gurbin sanatan Bayelsa Central and West. Kakakin 'yansandan jihar, Asinim Butswat ne ya tabbatar da faruwar lamarin. Saidai ya gayawa Puch cewa basu tantance yawan wanda suka rasu ba. “The boat capsized on their way to Oporoma, headquarters of Southern Ijaw Local Government Area,”he said.
Haramtacciyar Matatar mai: Fashewar iskar gas ya ci rayukan mutane uku a Bayelsa

Haramtacciyar Matatar mai: Fashewar iskar gas ya ci rayukan mutane uku a Bayelsa

Uncategorized
Mun samu rahoton mutuwar wasu matasa uku a wani haramtaccen sansanin matatar mai wanda ke tsakanin garin Ibelebiri da Otuegue 2 a karamar hukumar Ogia da ke jihar Bayelsa, bayan fashewar iskar gas.   Wasu da yawa an ce sun samu rauni iri daban-daban yayin lamarin. Wadanda suka mutu sun hada da Victory Friday, Endurance Glazio da James Abaye. Lamarin, kamar yadda jaridar Vanguard ta samu labarin ta faru ne a ranar Alhamis da misalin karfe 11 na dare a haramtacciyar matatar matatar wacce aka fi sani da Kpo-fire camp da ke can cikin wani wuri mai zurfin fadama.
Yan Bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa da kuma kashe dansanda

Yan Bindiga sun kai hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa da kuma kashe dansanda

Uncategorized
Yan Bindiga sun kai Hari gidan tsohon gwamnan Bayelsa, Seriake Dickson inda suka harbi dansandan dake gadin gidan.   Lamarin ya farune a Toru-Orua dake karamar hukumar Sagbama a jihar. Yan Bindigar sun kai harinne da safiyar yau inda suka biyo ta ruwa.   Kakakin tsohon gwamnan, Fidelis Soriwei ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma mutuwar dansandan. Kakakin 'yansandan jihar, Asinim Butswat ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za'a fitar da sanarwa kan faruwar lamarin.
Da Duminsa: Kotu ta tabbatar da Douye Diri a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa

Da Duminsa: Kotu ta tabbatar da Douye Diri a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa

Siyasa
Alkalai 7 na kotun koli sun tabbatar da Douye Diri a matsayin zababben gwamnan jihar Bayelsa.   Mai shari'a, Sylvester Ngwuta ne ya tabbatar da hakan inda yayi watsi da korafe-korafe 7 da aka shigar na kalubalantar Gwamna Diri da Mataimakinsa, Lawrence. Diri na jam'iyyar PDP ya zo a masayin na 2 ne a zaben inda kuma bayan da kotu ta cire David Lyon na jam'iyyar APC ta bashi mukamin gwamnan.
Magoya bayan APC sun bazama kan tituna suna murnar soke zaben gwamnan Bayelsa

Magoya bayan APC sun bazama kan tituna suna murnar soke zaben gwamnan Bayelsa

Siyasa
Magoya bayan jam'iyyar APC a Birnin Yenagoa na jihar Bayelsa sun bazama kan tituna inda suka rika nuna murna da soke zaben gwamnan jihar da kotun sauraren kararrakin zabe ta yi.   Kotun ta soke zaben gwamna Duoye Diri saboda rashin saka jam'iyyar ANDP da dan takararta, a zaben da aka yi na 16 ga watan Nuwamba 2019. Kotun ta kuma bukaci da hukumar zabe me zaman kanta, INEC data hanzarta shirya wani zaben nan da kwanaki 90.   Dan takarar jam'iyyar APC, David Lyon ne ya yayi nasara a zaben amma daga baya kotu ta kwace zaben ta baiwa dan PDP saboda samun mataimakin Lyon da takardar karatu ta Bogi.   Tuni dai gwamna Diri ya baiwa Lauyansa Umarnin a daukaka karan.
Har yanzu Diri ne gwamnan Bayelsa>>Dickson

Har yanzu Diri ne gwamnan Bayelsa>>Dickson

Siyasa
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson ya bayyana cew har yanzu gwamna Duoye Diri ne gwamnan jihar duk da soke zaben da Kotu ta yi.   Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa. Yace sai kotun koli ta kammala shari'a sannan za'a san wane mataki ya kamata a dauka saboda yanzu akwai damar daukaka kara. Dickson ya bayyanawa jama'ar jihar cewa kada su yi kasa a gwiwa su ci gaba da harkokinsu domin gwamnan nasu yana nan daram.
Yanzu-Yanzu:Kotu ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa

Yanzu-Yanzu:Kotu ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa

Siyasa
Kotun sauraren kararrakin zabe ta musamman dake da zama a Abuja ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa, Duye Diri a yau Litinin.   Zaman Kotun da maishari'a, Muhammad Sirajo ya jagoranci alkalai 3 sun yanke hukuncin cewa zaben ya haramta saboda ba'a saka jam'iyyar  AND da dantakarar ta a zaben da ya gudana ranar 16 ga watan Nuwamba 2019 ba. Kotun ta bukaci hukumar zabe me zaman kanta, INEC dsta shirya wani zaben nan da kwanaki 90
Jihar Bayelsa ta bude gurren Ibada

Jihar Bayelsa ta bude gurren Ibada

Uncategorized
Rahotanni daga jihar Bayelsa na cewa jihar ta Bude guraren Ibada inda ta baiwa coci-coci masu manyan gine-gine su rika ibada da mutanen da basu wuce 200 ba. Wannan na kunshene cikin sanarwar da shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 na jihar, Bangaren Coci, Fasto Samuel John Peters.   Sanarwar tace amm coci-coci ya zamana suna bin dokar nesa-nesa da juna da kuma samar da abin wanke hannu