fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Bayer Munich

Bayern Munich ta cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai sau 19, fiye da kowace kungiya a tarihin gasar

Bayern Munich ta cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai sau 19, fiye da kowace kungiya a tarihin gasar

Wasanni
Kungiyar Bayern Munich ta cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai bayan ta lallasa Lazio daci 2-1 a jiya, inda doke ta daci 6-2 kenan a wasannin gida da waje. Bayern ta lallasa Lazio daci 4-1 a wasan waje da suka fara bugawa a Rome, inda kuma a jiya Robert Lewandowsku yaci mata bugun daga kai sai mai tsaron raga, wadda ta kasance kwallon shi ta 39 a wannan kakar. Kungiyar Jamus din ta kara zira kwallo guda a wasan ta hannun Choupo-Moting wanda ya musanyi Lewandowski kafin Lazio ta rama guda ta hannu Marco Porolo. A karshe dai sakamakon wasan yasa yanzu Bayern Munich ta zamo kungiya ta farko data cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe sau 19 a tarihin gasar zakarun nahiyar turai. 19 - Bayern Munich have reached the quarter-fin...
Bayern Munich ta daga kofin German Super Cup bayan ta lallasa Dortmund 3-2

Bayern Munich ta daga kofin German Super Cup bayan ta lallasa Dortmund 3-2

Wasanni
Kungiyar zakarun kasar Jamus, Bayern Munich ta lashe kofi na biyar a wannan shekarar a wasan data buga da Dortmund daren yau a filin tana Allianze Arena wanda suka yi nasarar tashi 3-2 bayan Joshua Kimmich ya zira kwallon ana gab da tashi wasan kuma suka daga kofin German Super Cup. Bayern Munich ta fara jagorantar wasan da kwallaye biyu ta hannun Corentin Tolisso da kuma Thomas Muller kafin Julian Brandit ya ramawa Dortmund kwallo guda ana gab da zuwa hutun rabin lokaci, kuma bayan an dawo daga hutun zakaran Dortmund Erling Braut Haaland ya kara zira kwallo guda wadda tasa suka kasance 2-2 amma Kimmich ya zira kwallo ana gab da tashi wadda tasa Bayern suka lashe kofin. Dortmund ta buga wasan ne ba tare da tauraron ta ba wanda Manchester United take farauta wato Jadon Sancho kuma...
Hoffenheim 4-1 Bayern Munich: Yayin da Munich ta fadi wasa karo na farko tun 2019

Hoffenheim 4-1 Bayern Munich: Yayin da Munich ta fadi wasa karo na farko tun 2019

Wasanni
Kungiyar zakarun kasar Jamus wadda ta yi nasarar lashe kofuna hudu a kakar data gabata, Bayern Munich ta sha kashi a hannun Hoffenheim yau a gasar Bundlesliga yayin da kungiyar ta dakatar da Munich bayan tayi nasarar buga wasanni 32 ba tare da an cire ta ba tun shekarar data gabata. Bayern Munich, wadda tayi nasarar lashe kofin UEFA ranar alhamis tsakanin tada Sevilla bata fadi wasa ko guda ba tun 7 ga watan disemba na 2019 kuma ta buga wasanni 21 na Bundlesliga a jere ba tare da an ci taba yayin da kuma ita taci wasannin tana gasar guda 15 da suka gabata. Hoffenheim taci Munich kwallaye biyu cikin mintina 8 ta hannun Ermin Biacakcic da kuma Munus Dabbur kafin Joshua Kmmich ta ramawa Munich kwallo guda bayan ta kai hare-hare masu kyauta hannun gwarazan yan wasan ta. Amma kwallon ...
Bayer Munich ta kai wasan karshe na gasar Champions League bayan lallasa Lyon da 3-0

Bayer Munich ta kai wasan karshe na gasar Champions League bayan lallasa Lyon da 3-0

Uncategorized
Kungiyar kwallon kafa ta Bayer Munich ta lallasa Lyon da ci 3-0 a wasan da suka yi a daren yau na kusa dana kusa dana karshe na gasar Champions League.   Gnabry ne ya fara jefawa Munich kwallaye 2 kamin tafiya hutun Rabin lokaci inda bayan dawowa, Robert Lewandowski ya jefa kwallo ta 3. Hutudole ya samo muku cewa wannan kwallo da Lewandowski yaci itace ta 15 da yaci a gasar Champions League na bana. Sannan kuma ya ci kwallo a duka wasannin da ya buga na gasar. Kwalaye 2 suka ragewa Lewandowski ya kamo Cristiano Ronaldo a tarihin da ya kafa na cin kwallaye mafiya yawa a gasar Champions League 1, watau 17.
Bayern Munich ta mayarwa tsohon dan wasan ta Vidal Martani bayan ta kafa tarihin mamaki akan Barcelona

Bayern Munich ta mayarwa tsohon dan wasan ta Vidal Martani bayan ta kafa tarihin mamaki akan Barcelona

Wasanni
Bayern Munich ta kafa sabon tarihi a gasar Champions League yayin da ta zamo kungiya ta farko data ci kwallaye takwas a wasan quarter final na gasar. kuma wannan tarihin ya dauki hankula sosai saboda akan daya daga cikin manyan kungiyoyin wasan kwallon kafa ta kafa tarihin wato Barcelona kuma Messi yana cikin wasan amma ya kasa kare kungiyar tashi. Tsohon dan wasan Bayern Munichi kuma tauraron Barcelona Arturo Vidal yayi wani jawabi kafin a buga wasan yayin da yake cewa ya kamata Munich ta san cewa wannan karin da Barcelona zata buga wasa bada kungyar Bundlesliga ba. kuma Munich ta bashi kyakkawar amsa yayin data lallasa kungiyar tashi har 8-2 kuma Vidal bai ci ko kwallo guda ba. Muller ya gargadi abokan aikin shi kafin a buga wasan yayin da yake cewa idan har suna so su dakata...
Hoto: Yanda Lionel Messi ya ware kansa daga sauran ‘yan wasan Barcelona bayan ci 8-2 da Bayer Munich ta musu

Hoto: Yanda Lionel Messi ya ware kansa daga sauran ‘yan wasan Barcelona bayan ci 8-2 da Bayer Munich ta musu

Wasanni
Bayan kammala wasan daren jiya da Bayer Munich ta wa Barcelona 8-2 na gasar cin kofin Champions League.  Tauaron Barcelona,  Lionel Messi ya kasa shiga cikin sauran Abokan wasanshi.   Da aka koma dakin canja Kaya, Messi ya koma gefe guda inda ya rika jimamin abinda ya faru dasu. Hutudole ya ruwaito muku cewa Messi ya kasa tseratar da Barcelona daga abin kunyar da bayer Munich ta mata  
Champions League:Bayer Munich ce zata lallasa Barcelona>>Lothar Mattaus

Champions League:Bayer Munich ce zata lallasa Barcelona>>Lothar Mattaus

Wasanni
Lothar Matthaus baya tunanin Barcelona zata yi nasara akan Bayern Munich a wasan da zasu buga ranar juma'a. Barcelona zata kara da Munich a gasar zakarun nahiyar turai bayan ta cire Napoli a wasan da suka buga jiya wanda suka tashi 3-1, amma shi tsohon dan wasan jamus din ya bayyana a fili cewa Munich yake  tayi nasara a wasan. Lothar ya bayyanawa Sky Germany cewa tabbas Barcelona suna yin kokari sosai a wasannin su, amma sai dai yana tunanin cewa ba karamin kuskure Munich zata yi ba kuma ba karamin sakaci zata yi ba wanda har zai sa su fadi wasa tsakanin su da Barcelona. Ya kara da cewa amma sai dai wasu lokutan abubuwa sun kasancewa musamman a wasannin daba na 1st leg da 2nd leg ba, domin zaka iya gyara kuskuren da kayi a wasan 1st leg.Amma idan ba haka ba akwai wasannin dasu...
Kungiyar Munich, Juventus da Paris Saint German sune kadai kungiyoyin da zasu iya lashe kofunan gasa har guda uku

Kungiyar Munich, Juventus da Paris Saint German sune kadai kungiyoyin da zasu iya lashe kofunan gasa har guda uku

Wasanni
A ranar laraba kungiyar Bayern Munich suka yi nasara a wasa na kusa da karshe a gasar DFB-Pokal tsakanin su da Eintracht Frankfurt, kuma hakan ya nuna cewa kungiyar Munich din da PSG da Juventus ne kasai wa'yan da zasu iya lashe kofunan gasa har guda uku. Barcelona da Real Madrid baza su iya lashe kofunan gasa har guda uku ba yayin da aka cire su a gasar Copa del Rey, suma Manchester City baza su lashe kofin gasar Premier lig yayin da aka cire Liverpool a gasar Champions lig da FA Cup. Munich, Juventus da Paris Saint German sune kadai kungiyoyin da suke da damar lashe kofunan gasa har guda uku a kakar wasan bana, kuma gabadayan su sune a saman teburin gasar su ta kasa. Napoli suma suna cikin gasa har guda uku amma sai dai basu da alamar sa'a a gasar Serie A. An baiwa kungiya...