
Jami’ar Bayero dake Kano ta soke shekarar karatu ta 2019-2020
Jami'ar Bayero dake Kano ta sanar da soke Shekarar Karatu ta 2019-2020. Masu gudanarwa na jami'ar ne suka bayyana haka.
Sanarwar ta fito a yau daga registerar Makarantar, Fatima Bintu Muhammad inda hakan ke zuwa makwanni kadan bayan janye yajin aikin ASUU.
Jami'ar ta sanar da soke cewa sabuwar shekarar karatunta zata fara daga 18 ga watan Janairu na shekarar 2021, kamar yanda Dailytrust ta ruwaito.