fbpx
Thursday, February 9
Shadow

Tag: bbchausa.com

Burnley ta sayi golan Manchester City a kan fam miliyan 3.5

Uncategorized
Burnley ta sayi golan Manchester City Joe Hart a kwantaragin shekara biyu a kan fam miliyan 3.5. Shugaban kungiyar Sean Dyche ya sayi golan ne tare da saurarn gololi biyu wato Nick Pope da Tom Heaton. Hart, wanda ya yi wa kasar Ingila wasanni 75, ya kuma yi wa City wasanni 350, inda suka lashe kofin Firimiya biyu da kuma Kofin FA daya. Golan ya fara nuna sha'awar barin City ne tun bayan da Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya rika ajiye shi a benci. Sau daya Hart ya kama wa City gola tun bayan da Guardiola ya zama kocin kungiyar a shekarar 2016. Ya kuma kwashe kaka biyu a matsayin aro a kungiyar Torino da kuma West Ham. Hakazalika kasar Ingila ba ta je da shi gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha a shekarar 2018. BBChausa.

Mutane sun ga duniyoyin Venus da Jupiter a lokaci guda

Uncategorized
An ga Jupiter da Venus, duniyoyi biyu mafi haske, wadanda suka bayyana tare da juna a sararin samaniya da safe. Ana ganin su da ido a sassan Birtaniya da wasu kasashe da ke tsakiya da arewacin duniya, da kuma wani sashe na Amurka. Masana sun ce duniyoyin sun kasance kusa da juna, kamar wasu taurari masu haske. An fi ganinsu a Birtaniya, minti 40 kafin fitowar rana, amma duniyoyin suna fara bayyana ne kafin fitowar Al Fijir. A yayin da ake iya ganinsu da ido, wasu da suka yi amfani da na'urar hangen nesa na iya ganin wasu halittun duniyar Jupiter. Mutanen Birtaniya da dama sun yada hotunan yadda duniyoyin biyu suka bayyana a shafukan sadarwa na Intanet. bbchausa.

‘Mace za ta iya marin mijinta don Buhari’

Uncategorized
Shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Shittu Sh'aibu Shittu, ya ce taba Buhari a siyasar jihar wani abu ne mai wuya, inda ya ce matar wanda ya soki Buhari za ta iya marinsa. Alhaji Shittu ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake mayar da martani game da zargin da bangaren 'yan APC akida ke yi na cewa gwmanatin APC mai mulki a jihar ta saki hanyar cika alkawuran da jam'iyyar ta dauka wa al'ummar jihar. A hirarsa da Ibrahim Isa, shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina ya ce: "Wasu mutane ne da suka sha kayi a zabe. Suna ganin suna da damar da ya kamata a ce sun samu mukamai a gwamnatin tarayya, kuma Allah bai sa an samu ba, kuma ba su mayar da al'amarinsu ga Allah ba." Da aka tambayi dan siyasar cewa ko akwai wani shiri da gwmamnatin ke yi na janyo mutanen jiki. Sai ya ce...

Illar da ke tattare da tsoho ya auri karamar yarinya

Uncategorized
Jagorar mata a rundunar Hukumar Hisbah ta jihar Kano, Najeriya, Dr. Zahra'u Muhammad Umar, ta ce akwai matsala babba dangane da aurar da kananan yara mata ga tsofaffi. Ta ce duk da cewa batun tsoho ya auri karamar yarinya wani abu ne da tasha faman tattaunawa a kai, har ma kuma ta fafata da malaman addini masu kare irin wannan muradi. Kusan za a iya cewa auren karamar yarinya ga tsaffi wani batu ne da ba kasafai ake tattauna shi ba sakamakon rashin haramcinsa a addini da al'ada. To sai dai Dr Zahra'u ta ce duk da cewa addini bai haramta irin wannan aure ba amma zamani da irin illolin da ke tattare da wannan aure ka iya sa a sanya masa ayar tambaya. bbchausa.

Yadda ‘yar shekara 80 ta zagaye kasashen Afirka a mota

Uncategorized
A yayin da mutum ya kai shekara 80 a duniya, wani zai yi tunanin lokaci ya yi ya daina wasu abubuwa, sai dai batun ba haka yake ba ga wata dattijuwa Julia Albu 'yar kasar Afirka ta Kudu. Don kuwa a ranar da ta cika shekara 80 a duniya ne ta dauki 'yar tsohuwar motarta domin fara rangadi a nahiyar Afrika. Haka zalika ta dauki tanti da tukwane da kuma kayan sawa ne kafin ta dauki hanya a watan Yunin da ya gabata. Sai dai ta dawo Afirka ta Kudu inda take jiran bizarta ta zuwa Sudan kafin ta kara daukar hanya. Dattijuwar dai na rubuta bayanan abubuwan da ke faruwa a yayin wannan rangadi da suka hada da gudunmawar da ake bayarwa na wani shirin tallafi da take kira SHINE, wanda ake koyar da yara karatu. Wakilin BBC Mohammed Ali ya tambaye ta shin ko lokacin da za ta fara rangadin an ...

Banufe Umar ya auri inyamura A’ishat Obi

Uncategorized
A wannan lokacin da ake ganin kawunan kabilun kasarnan yana kara rarrabuwa wani abin birgewa da ban sha'awa ya faru inda wani Banufe da aka bayya sunanshi da Umar ya auri masoyiyarshi wadda inyamurace me suna A'isha Obi data fito daga jihar Imo. Saboda irin yanda suka birge mutane anyita sa musu albarka a shafukan sada zumunta da muhawara, muna muna musu fatan Allah ya yiwa wannan aure nasu albarka ya kuma kawo zuri'a ta garu.