
Kai da ake Luwadi da kai>>Dan gidan Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya gayawa Wani da ya caccaki mahaifinsa
Dan gidan gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya caccaki wani da ya soki mahaifinsa a shafin Twitter.
Elnathan John wanda shahararren Marubuci ne ya bayyana cewa gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai mutum ne me matukar hadari. Hutudole ya tattaro muku cewa Marubucin ya zargi gwamnan da yada karya da kuma daukar wasu suna masa irin wannan aiki.
Saidai dan gwamnan, Bello bayyana cewa shi wannan Marubuci ana Luwadi dashi dan a bashi takardar shedar zama dan kasar Jamus.
Dan uwansa, Bashir El-Rufai ya goya masa baya akan wannan caccaka da yawa marubucin.