fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Tag: Benin

Idan makwabcinka ya tsira kaima ka tsira>>Shugaba Buhari ya fada yayin ganawa da shugaban kasar Benin

Idan makwabcinka ya tsira kaima ka tsira>>Shugaba Buhari ya fada yayin ganawa da shugaban kasar Benin

Siyasa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa makwabtaka na da muhimmanci a rayuwar al'umma.   Yace idan makwabcinka ya tsira to kaima ka tsira, Hakanan idan ka tsira shima ya tsira. Ya bayhana hakane a fadarsa yayin karbar bakuncin shugaban kasar Benin, Patrice Talon a ziyarar da ya kawo Najeriya.   Shugaba Buhari ya bayyana cewa muhimmancin makwabtaka da kuma tsaro tsakanin kasashen yasa a shekarar 2015 da ya karbi mulki ya fara zagaya kasashen Africa dake makwabtaka da Najeriya san kamo bakin zaren.   Shima shugaba Talon ya bayyana cewa, ya zo Najeriya ne dan jinjinawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari bisa jagoranci na gari a Nahiyar Africa da Najeriya. YOUR NEIGHBOUR’S SURVIVAL IS ALSO YOUR OWN, PRESIDENT BUHARI TELLS VISITING BENIN REPUBLI...
Sarkin Benin ya taya Al’ummar Musulmi murnar Mauludi

Sarkin Benin ya taya Al’ummar Musulmi murnar Mauludi

Uncategorized
Sarkin Benin Akpolokpolo, Ewuare ya taya daukacin musulmai murnar zagayowar ranar mauludi, ranar da a ka hafi fiyayan halitta Annabi Muhammad tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gare shi. Sanarwar hakan na kunshe ne ta cikin sanarwar da sakataran yada labarai na sarkin ya fitar Mista Victor Ogiemwanre, inda ya bukaci musulmai da su cigaba da koyi da halaye da dabi'u na Annabi (S A W). A karshe ya ja hankalin daukacin al'ummar kasa baki daya da su zauna lafiya da juna.
Masu zanga-zangar SARS Sun tsare wani Helikwafta ‘Yan Sanda A Benin

Masu zanga-zangar SARS Sun tsare wani Helikwafta ‘Yan Sanda A Benin

Tsaro, Uncategorized
Mazauna garin Oluku da ke kusa da Benin, babban birnin jihar Edo sun tsare wani helikoftan ‘yan sanda da ya yi kuskuran sauka a wani fili a yankin da ke cike da masu zanga-zangar adawa da rundunar SARS. Mazauna garin Oluku, wadanda suka kewaye helikoftan, nan take suka yi da'awar cewa Jami'an tsaro sun zo ne domin su sanya musu ido game da ayyukan su a yankin yayin zanga-zangar #EndSARS. Jami'in hulda da jama'a na 'yan sanda na Edo (PPRO), Chidi Nwabuzor, bai ce komai ba game da lamarin.
Ban sa a zagi Buhari ba>>Sarkin Benin

Ban sa a zagi Buhari ba>>Sarkin Benin

Siyasa
Oba na Benin, Oba Ewuare II, ya nesanta kansa da zagin Shugaba Buhari a shafukan zumunta tare da wasu mutum biyu da ya ce jihar Edo na alfahari da su. Basaraken ya ce bai lamunce wa kowa zagin Buhari ko tsohon Gwamnan Jihar Edo Adams Oshiomhole ko Kaftin Hosa Okubor ba, abin da ya kira da aikin masu neman magana. “Muna allawadai da babbar murya game da cinn mutunci da aka yi wa Shugaba Buhari da sauran mutanen da bidiyon ya ambata”, inji Masarautar Benin. Basaraken na martani ne ga wani bidiyo a shafukan zumunta, wanda a ciki wani mai suna Eranomigho Edegbe, ya ce Oban ya ba shi izini zagin Buhari da mutanen. Obar Ewuare II, ya bukaci Eranomigho da ya nemi afuwarsa daga mummuan aikin da ya yi da ya zubar da kimar Masarautar ta Benin. Sanarwar da Sakataren Majalisar...
Shugaba Buhari ya bayyana matsayinsa kan sake bude iyakokin Najeriya

Shugaba Buhari ya bayyana matsayinsa kan sake bude iyakokin Najeriya

Siyasa
A ranar Talata, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin gwamnatinsa a shirye take ta aiwatar da shawarar kwamitin sulhu a kan rufe wasu hanyoyin iyakokin kasarnan. Kwamitin ya hada da Najeriya, Benin da Nijar.  A ganawara da Mista Bashir Mamman Ifo, shugaban bankin ECOWAS na zuba jari da ci gaba (EBID) da wanda zai gaje shi, Dakta George Nana Donkor, da ya yi a Abuja, Buhari ya yi bayanin cewa rufe iyakokin na wucin gadi ya baiwa Najeriya dumbin nasarori. Shugaba Buhari ya bayyana dumbin Nasarori da hakan ya haifarwa Najeriya, Inda ya kara da cewa, tattalin Najeriya ya habaka, Najeriya ta dogara da kanta wajan Samar da abinci.  "Mun hana shigo da muggan kwayoyi da kuma yaduwar kananan makamai wadanda ke barazana ga kasarmu," in ji Shugaban. Buhari ...