
Matt Hummels yaci gida yayin da zakarun duniya Faransa ta doke Jamus daci 1-0 a gasar Euro
Hummels, wanda kocin Jamus Joachim Low ya kira ya buga nasa wasa karo na farko cikin shekaru biyu yayi kuskuren cin gida a minti na 20 yayin cire kwallon da Lucas Hernandez ya bugo.
Serge Gnabry ya kusa ramawa Jamus kwallon da taimakon Robin Gosens, yayin da ita kuma tawagar Didier Deschamps ta kara karfi sakamakon dawowar Benzema.
Kuma tauraron Madrid din tare da Mbappe duk sunci kwallaye amma aka soke sakamakon offside, yayin da nasarar da suka yi tasa makin su yayi daidai dana Portugal wadda ta doke Hungary daci 3-0 a group F kuma ta bar Jamus da babban aiki a gabanta.
Yayin da shi kuma Antonio Rudiger yayi yunkurin cizon Pogba a wasan idan tauraron United ya kai kara wurin alkalin wasa amma duk da haka alkalin bai dau wani mataki ba.
France 1-0 Germany: Mats Hummels' own ...