fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Bet9ja

Ya kashe kanshi bayan da ya buga caca da kudin me gidanshi Dubu 150 kuma aka cinyesu

Ya kashe kanshi bayan da ya buga caca da kudin me gidanshi Dubu 150 kuma aka cinyesu

Uncategorized
Wani matashi me kimanin shekaru 28 ya kashe kanshi bayan da yayi amfani da kudin me gidanshi har Naira Dubu 150 ya buga cacar Bet 9ja kuma aka cinyesu.   Matashin daya fito daga karamar hukumar Nembe ta jihar Bayelsa an bayyana cewa ya sha maganin kwarine ya mutu. Matashin me suna Suga an bayyana cewa yana yiwa ogan nasa tsaron shagon cacarne wanda bayan yayi cacar kudin suka dulmuye gashi kuma bai san me zai gayawa ogan nasa ba kawai ya kashe kanshi.   Me magana da yawun 'yansandan jihar Asinim Batswat ya bayyana cewa sun san da lamarin amma ba a kawo musu korafi ba a hukumance.