
Gwamnatin tarayya ta bada hutu Ranekun Litinin da Talata dan Bikin Sallah
Gwamnatin tarayya ta bayyana ranekun Litinin da Talata a matsayin ranekun hutun bikin sallah karama.
Hakan ya fitone daga bakin ministan harkokin cikin gida,Ogbeni Rauf Aregbesola ta bakin me magana da yawun ma'aikatar, Munammad Manga a yau,Alhamis.
Yace yana taya daukacin musulmai murnar kammala azumin watan Ramadana.
Yayi kira ga musulmai da su ci gaba da amfani da kyawawan halayen da aka yi a Ramadana na Kirki, tausayi, Hakuri, soyayya, Zaman Lafiya da kyakkyawar makwautaka har bayan Ramadana dan Koyi da Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad(SAW).