
Gwamna Ganduje ya baiwa tsohuwar Hadimar Kwakwaso mukami a gwamnatinsa
Rahotanni daga jihar Kano na cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya baiwa Binta Rabiu Spikin mukami a gwamnatinsa.
Majiyarmu ta Independent ta bayyana cewa gwamna Ganduje ya baiwa Spikin mukamin mataimakiya ta musamman kan bincke.
Binta, tsohuwar me magana da yawun tsohon gwamnan kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce wadda ta raba gari dashi ta koma APC.