fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

Tag: Binuwai

Kishi ya sanya wani Mutum bankawa kansa wuta da budurwarsa A Jihar Binuwai

Kishi ya sanya wani Mutum bankawa kansa wuta da budurwarsa A Jihar Binuwai

Crime
Rundunar 'yan sandan jihar Binuwai ta ce, ta samu rahoton mutuwar wani mutum mai suna Nicodemus bisa zargin cinnawa kansa wuta tare da Budurwarsa wanda yayi sanadin Ajalinsu. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar DSP Catherine Anene, ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) cewa, Matashin ya mutu nan take, yayin da budurwar, wacce aka bayyana da suna Shiminenge, ta mutu daga baya a Asibitin Koyarwa na Jihar Benuwai. Kakakin ta kuma bayyana cewa, Nicodemus ya aikata wannan aika-aikar ne a gidan budurwar tasa da ke kan titin Inkipi, a garin Makurdi da yammacin ranar Asabar. Inda ta shaida cewa, An samu sabani a tsakanin masoyan biyu, sai dai ta ce, harzuwa yanzu basu kai ga gano musabbabin rikicin ba. Hakanan Ta kuma kara da cewa, Matashin ya kulle kansa ne da masoy...