Rahama Sadau ta taya kakkyawar kanwarta murnar zagayowar ranar haihuwarta
Tauraruwar fina-finan hausa da turanci, Rahama Sadau ta taya daya daga cikin kyawawan kannen ta, Zainab Sadau murnar zagayowar ranar haihuwarta.
Rahamar ta saka hotunan 'yar uwartata a dandalin sada zumunta da muhawara inda ta mata fatan alheri.
Muna tayata murna da fatan Allah ya karo shekaru masu Albarka.