
Da Duminsa: ‘Yan Bindiga sun budewa tawagar Motar sarkin Birnin Gwari wuta
'Yan Bindiga sun budewa tawagar motocin sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari na II wuta.
Lamarin ya farune akan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, saidai Sarkin baya cikin tawagar motocin.
Direbansa, Umar Jibril ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna tafiya suka ga 'yan Bindigar sun ajiye itace akan hanya, yace kawai sai basu tsaya ba suka shigesu, yace sun yi ta harbi Amma Allah ya tsaresu, in banda kananan raunuka na Fashewar Gilashi, babu abinda ya samesu.
“We did not stop, they targeted me, since I was driving but as Allah will have it, the bullet missed my head.”