
Shekaru 5 da suka gabata ne mafiya muni a tarihin Najeriya>>Bishop Oyedepo
Shugaban cocin Living Faith, Bishop David Oyedepo ya bayyana cewa shekaru 5 da suka gaba ne mafiya muni a tarihin Najeriya.
Ya bayyana goyon bayansa ga zanga-zangar da matasa ke yi na EndSARS inda yace kowa yana da damar ya fita ya bayyana ra'ayinsa.
Yace bai fito yayi magana bane saboda a shekarar 2015 sai da ya gargadi 'yan Najeriya akan abinda ke faruwa yanzu amma aka ki ji. Yace duk gwamnatin da bata san darajar rayukan mutane ba bata da amfani. Su da an kashesu lokacin suna matasa zasu kai matsayin da suke a yanzu?
Yace ba zaka san Akuya na da hakora ba sai ka kaita bango tukuna.
“Every man has a right, legitimately so, to express their displeasure and pains
I kept quiet for a while because in 2015 I warned this nation, vehemently, cons...