fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Boeing

Kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya sallami ma’aikata

Kamfanin kera jiragen sama na Boeing ya sallami ma’aikata

Kasuwanci
Kamfanin kera jiragen sama na Boeing, ya ce zai rage ma'aikata da za su kai kashi 10%, bayan ya sanar da asarar dala miliyan 641 a watanni uku na farkon wannan shekara, saboda illar da corona ta yi masa. Haka nan zai dakatar da wasu daga cikin manyan jiragen jigilar fasinjoji da yake kerawa da suka hada da samfurin 787 da kuma 777. A baya dai kamfanin na samun ribar sama da dala biliyan biyu. A bayyana take dai harkokin surufin sama, za su kwashe shekaru kafin sake komawa yanda aka saba, don haka ne shugaban kamfanin, David Calhoun, ke cewa tilas ne a shirya wa yanayin. Dama dai kamfanin na da ma'aikata dubu 160 ne, abin da a yanzu zai shafi mutum dubu 16 ke nan.