
Labari me dadi: Yan Boko-Haram guda 15 sun mika tuba sun mika wuya ga rundunar sojin Najeriya tare da makamansu
Yan ta'addan Boko-Haram da yan ISWAP guda 15 sun tuba sun mika wuya ga rundunar sojin Najeriya tare da makamansu.
Manazarcin tsaro, Zangola Makama ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter inda yace yan ta'adn sun muka wuya ne a jihar Borno.
Kuma daga cikin su akwai balagaggun mazaje guda goma da kuma yara guda biyar, yayin da yace sun mika wuyan ne ga rundunar sojin dake karamar hukumar Bama a jihar ta Borno.