
Aishwarya Rai da diyarta sun kamu da Coronavirus/COVID-19
Rahotanni daga kasar India na cewa Aishwarya Rai da diyarta Aaradhya ma sun kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.
Wata majiya a kasar ce ta gayawa kamfabin dillancin labaran AFP haka, hakan na zuwa kwana 1 bayan da Surukin Aishwarya, Amitabh Bachchan da Dansa, Abhishek suka kamu da cutar.