
Jihar Borno ta sallami karin mutum 10 wanda suka warke daga cutar coronavirus/covid-19
A ranar Alhamis ma'aikatar lafiya dake jihar Borno ta tabbatar da sallamar mutum 10 Wanda suka warke daga cutar covid-19, Wanda ya kawo adadin mutum 185 da aka sallama a jihar.
Baya ga haka cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta fidda sanarwar samun Karin mutum 26 wanda suka harbu da cutar a jihar.
https://twitter.com/Borno_Health/status/1268676651862437890?s=20
Sai dai a zuwa yanzu jihar nada adadin mutum 322 masu dauke da cutar coronavirus, yayin da mutum 26 suka mutu a sakamakon cutar.