
Ortom, Shehu Sani Sun yi Allah wadai da Harin Da aka kai kan Ayarin Motoci gwamna Zulum
Gwamnan jihar Benuwe , Samuel Ortom ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa jerin gwanon motocin takwaran sa na jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, yana mai bayyana harin a matsayin abin firgici da takaici.
Gwamnan ya kuma bayyana kwarin gwiwar sa kan cewa "Gwamna Zulum ba zai yi kasa a gwiwa ba wajan ci gaba da aiki tare da jami'an tsaro don maido da zaman lafiya a dukkan sassan jiharsa."
Shi ma da yake mayar da martani ta shafinsa na twitter, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi kira ga Gwamna Zulum da ya yi taka-tsantsan a wuraren da har yanzu ke fama da rikicin Boko Haram.