Friday, May 29
Shadow

Tag: Borno

BABBAR NASARA DAGA ALLAH: Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Da Dama A Jihar Borno

BABBAR NASARA DAGA ALLAH: Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Boko Haram Da Dama A Jihar Borno

Tsaro
Dakarun sojin Nijeriya mazajen fama, sojojin kundunbala, rundinar Janar Buratai sun samu nasarar kutsawa wani babban sansanin 'yan ta'addan Boko Haram dake Gomborou inda suka yi wa 'yan ta'addan kofar rago.     Adadi mai yawa na 'yan ta'addan Boko Haram sun bakunci lahira, an kubutar da mata da yara kanana sama da 100, jaruman sojojin sun cire tutar 'yan ta'addan sun maye gurbinta da tutar Nijeriya.   Ai dama duk 'dan da yace uwarsa ba za ta yi bacci ba, to shi ma ba zai yi ba, 'yan Boko Haram mu je zuwa dan ubanku, shege ka fasa!     Yaa Allah Ka taimaki rundinar sojin Nigeria, Ka tabbatar musu da cikakken nasara akan Boko Haram Amin. Datti Assalafiy
Kalli kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 da Dan majalisar Borno, Ahmad Satomi ya baiwa mutanensa

Kalli kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 da Dan majalisar Borno, Ahmad Satomi ya baiwa mutanensa

Uncategorized
Dan majalisar tarayya daga jihar Borno,Injiniya Ahmad Satomi ya baiwa jama'arsa tallafin kayan abinci dan saukaka musu radadin matsin tattalin arzikin da Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ta jefasu ciki.   Wannan ne kusan karo na 3 da yake baiwa jama'arsa tallafin inda magidanta maza da mata suka amfana.       https://twitter.com/OfficialBorno/status/1263398748173950976?s=19  
Gwamna Zulum ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin Borno saidai ya iske shuwagabannin kananan hukumomin basa bakin aiki

Gwamna Zulum ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin Borno saidai ya iske shuwagabannin kananan hukumomin basa bakin aiki

Siyasa
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa ya kai ziyarar ba zata kananan hukumomin jihar 6 inda ya iske shuwagabannin kananan hukomomin basa bakin aiki.   Sanarwar ta bayyana cewa hakan ya farune duk da cewa sati 2 da suka gabata gwamnan ya bada umarnin a dawo a ci gaba da aiki. Yace dama tun kamun zuwan Coronavirus/COVID-19 ya samu rahotannin cewa shuwagabannin kananan hukumomin Askira-Uba, Bama, Gwoza, Damboa da Chibok basa zuwa wajan aiki, a Maiduguri suke zaune sai idan za'a kaiwa kananan hukumomin kasonsu ko kuma zai kai ziyarane suke zuwa.   Yace yayi gargadi akan hakan inda ya bukaci shuwagabannin kananan hukumomin su rika kasancewa a kananan hukumominsu dan mutane su san ana yi dasu amma ga dukkan alamu basu ji gargadin nashi ba, yace dan...
Bamabamai 2 sun tashi Konduga, Jihar Borno da yammacin yau

Bamabamai 2 sun tashi Konduga, Jihar Borno da yammacin yau

Tsaro
Bayan dogon lokaci ba'aji duriyar Bamba, Rahotanni daga Yankin Konduga na jihar Borno na cewa bama bamai 2 ne suka tashi da misalin karfe 8 na yammacin yau Litinin.   Ba dai a bayyana ainahin barnar da bamabaman suka yi ba amma wata majiya tace akalla mutun 2 sun rasu.   Wata Majiyar tsaro ta gayawa Sahara Reporters cewa, mutane sama da 2 sun rasu.
Zulum ya bada umarnin biyan albashin watan Mayu a Borno

Zulum ya bada umarnin biyan albashin watan Mayu a Borno

Siyasa
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya amince da a biya albashin watan Mayu da kuma fansho domin ba ma'aikata damar yin shirye-shiryen sallah. Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a ta hannun mai taimaka masa kan watsa labarai Isa Gusau. Gwamnan ya bayyana cewa biyan albashin da wuri zai ba ma'aikata damar sayen kayayyaki da wuri domin gudun hauhawar farashi a lokacin sallah.
Makamai Sun Fada Gidajen Jama’a Sakamakon Fafatawa Da Boko Haram A Maiduguri

Makamai Sun Fada Gidajen Jama’a Sakamakon Fafatawa Da Boko Haram A Maiduguri

Tsaro
Sakamakon wata arangama tsakanin jami'an sojin Najeriya da wasu da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, wasu makamai sun fada kan wasu gidaje biyu a anguwar Bintu Suga dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.     Jami’an sojin Najeriya sun ce sun samu nasarar kashe wasu 'yan Boko Haram su 9, tare da kwace makamai 2.   Wani mazunin unguwar Binta Suga Muhammad Musa wanda lamarin ya shafa, ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa yana zaune a kofar gidansa da misalin karfe shida da kusan minti talatin, yaga wata wuta daga sama ta taso ta fada cikin gidan sa, amma babu wanda ya mutu ko ya sami wani rauni. Sannan ya ce jami’an ‘yan Sanda da Soji duka sun zo sun duba yanayin.   Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin Najeriya Kanal Sagir Musa ya
Jihar Borno tace a Ci gaba da Sallah sannan ta cire dokar hana zirga-zirga gaba daya

Jihar Borno tace a Ci gaba da Sallah sannan ta cire dokar hana zirga-zirga gaba daya

Uncategorized
Jihar Borno ta bayyana cewa ta dage dokar hana zirga-zirga gaba daya sannan kuma za'a ci gaba da Sallah.   Wannan sanarwar ta fitone daga bakin mataimakin gwamnan jihar, Usman Unar Kadafur a ganawar da yayi da manema labarai jiya Laraba.   Ya bayyana cewa an dage dokar hana zirga-zirga amma kuma ya jawo hankalin jama'ar jihar da su bi dokokin da aka gindaya dan dakile yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Ya kuma godew jama'ar jihar bisa hadin kan da suka bayar a dokar hana zirga-zirga da aka saka wadda ta yi tsawon mako 3.   Ya kuma ce za'a ci gaba da salloli 5 sannan coci-coci zasu ci gaba da Ibada amma yana kira ga shuwagabannin addinin da su tabbatar ana bin dokar saka abin rufe fuska da hanci da kuma nesa-nesa da juna.   Yace ...
Muryar shugaban Boko Haram, Shekau ta bayyana yana kuka yana rokon Allah tsari daga Harin Sojin Najeriya

Muryar shugaban Boko Haram, Shekau ta bayyana yana kuka yana rokon Allah tsari daga Harin Sojin Najeriya

Tsaro
Muryar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ta bayyana kamar yanda Daily Nigerian ta samu inda yayi magana da yaren Kanuri.   Shekau yayi kuka a cikin muryar da yayi magana inda ya rika rokon Allah ya tsareshi daga hare-haren sojojin Najeriya.   Sojojin Najeriya dai sun tsananta hare-haren akan kungiyar Boko Haram inda har shugaban sojin,Janar Tukur Yusuf Buratai ya koma Yankin Arewa Maso gabas da zama dan ya tabbatar an gama da kungiyar.   An ji shekau na cewa,Sun bar Izala, sun bar Tijjaniyya, sun bar shi'a inda suka koma gefe dan su yi ainahin ibadar Allah, suna rokon Allah ya tsaresu daga sharrin Sojojin Najeriyar.   Da yake sharhi akan wannan murya data bayyana, Bulama Bukarti wanda Lauyane kuma dan rajin kare hakkin Bil'adama w...
Sojojin Najeriya sun kashe Boko Haram 20

Sojojin Najeriya sun kashe Boko Haram 20

Tsaro
Rahotanni daga Jihar Borno na cewa dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da Mayakan Boko Haram a hanyar Gwoza zuwa Bama kuma sun kashe Boko Haram din 20.   Boko Haran sun kaiwa sojojin harin kwantan Baunane a yayin da sukewa Kantoman karanar hukumar Gwoza, Saeed Sambo rakiya.   Da yake hira da manema labarai a Maiduguri, yau Lahadi,Sambo ya bayyana cewa a jiya,Asabar da misalin karfe 10 na safe lamarin ya faru inda Boko Haram din suka jefawa Sojojin abin fashewa.   Yace sojojin sun mayarwa da Boko Haram martani inda suka fatattakesu, yace 20 daga cikin Boko Haram din sun bakunci Lahira inda wasu kuma suka ranta a na kare.   Ya kara da cewa, sojojin 6, Sgt. Onu Oga, Cpl. Jonah Inji, Lcpls. Dauda Isa da Lawal Yahaya, Cpl. Oku Sunday da Prt. Aust...