fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Boss Mustapha

Ku shiryawa zuwan Coronavirus/COVID-19 zagaye na 2>>Boss Mustapha

Ku shiryawa zuwan Coronavirus/COVID-19 zagaye na 2>>Boss Mustapha

Uncategorized
Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin dake yaki da cutar Coronavirus/COVID-19,  Boss Mustapha ya bayyanawa 'yan Najeeiya cewa su shiryawa zuwan cutar Coronavirus/COVID-19, zagaye na 2.   Boss Mustapha ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai inda yace yana farin ciki ganin cewa al'amura na dawo dadai. Yace amma fa sai an kiyaye dan kuwa akwai yiyuwar dawowar cutar Coronavirus/COVID-19 a karo na 2 idan ba a yi taka tsansan ba.   Yace hakan ya faru a kasashe da yawa duk da dai ba'a fatab ya faru a Najeriya amma dolene a kasance cikin shirin hakan.   COVID-19: Nigerians to anticipate second wave – PTF Mr Boss Mustapha, Chairman, Presidential Task Force (PTF) on COVID-19 has said that Nigerians should anticipate a second wave of t...
Osinbajo na son ci gaban zaman Najeriya a matsayin kasa daya>>Boss Mustapha

Osinbajo na son ci gaban zaman Najeriya a matsayin kasa daya>>Boss Mustapha

Siyasa
Sakatarwn gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya nesanta mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da cewa wai baya son ci gaban zaman Najeeiya a matsayin kasa daya.   Boss Mustapha ya bayyana hakane a wajan wani taro kan cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yanci  kai da aka yi a Abuja. Yace shugaban kasa, Muhammadu Buhari na son ci gaban kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya. Hakanan shima mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo hakan take.   Ya bayyana cewa shima a matsayinsa na sakataren gwamnatin tarayya yana son ci gaba da kasancewar Najeriyar a matsayin kasa daya.
CORONA: Akwai Yiwuwar Sake Kakaba Dokar Kulle A Najeriya>>Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustafah

CORONA: Akwai Yiwuwar Sake Kakaba Dokar Kulle A Najeriya>>Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustafah

Uncategorized
A daidai lokacin da wasu jihohi suka sake bude makarantun firamare da sakandire, Gwamnatin Tarayya ta yi kira da su kara yin taka-tsantsan saboda kauce wa barazanar sake barkewar cutar COVID-19.     Tuni dai aka sake bude makarantu a jihohin Legas, Ekiti da kuma Ogun, yayin da wasu da dama kuma suka saka ranakun komawar. Sai dai gwamnatin ta yi gargadin cewa in ba a yi aiki da lura ba, sake bude makarantun, dawo da sufurin jirage na kasa da kasa da sauran abubuwa na iya mayar da hannun agogo baya kan irin nasarorin da yanzu haka aka samu kan yaki da cutar.   Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana da Shugaban Kasa ya kafa na yaki da cutar, Boss Mustapha shi ne ya yi gargadin yayin jawabin kwamitin a Abuja ranar Litinin.  ...
Gwamnati ta ware Tiriliyan 2.6 dan tallafawa ‘yan kasuwa, ku yi amfani da wannan damar>>Boss Mustapha

Gwamnati ta ware Tiriliyan 2.6 dan tallafawa ‘yan kasuwa, ku yi amfani da wannan damar>>Boss Mustapha

Siyasa
Sakataren gwamnatin tarayya wanda kuma shine shugaban kwamitin gwamnatin tarayya dake kula da yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ware Tiriyan 2.6 dan baiwa 'yan kasuwa da sauran harkokin tattalin arziki tallafi saboda zuwa Coronavirus/COVID-19.   Boss Mustapha ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai inda ya jawo hankalin mutane su yi amfani da wannan damar. Hutudole ya ruwaito muku cewa, Boss Mustapha ya godewa matasa saboda yanda suke bada hadin kai wajan yaki da cutar Coronavirus/COVID-19. Ya bayyana cewa idan aka ci gana da samun irin wannan hafin kai, za'a yi nasara a yaki da cutar.
Najeriya ka iya fadawa wata sabuwar Annoba>>Sakataren Gwamnatin tarayya

Najeriya ka iya fadawa wata sabuwar Annoba>>Sakataren Gwamnatin tarayya

Siyasa
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa, Najeriya ka iya fadawa wata sabuwar annoba muddin bata dauki darasi daga abinda ya faru na Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 ba.   Boss Mustapha ya bayyana hakane yayin da yake ganawa da yake kaddamar da kwamitin kwararru akan kiwon Lafiya da zasu duba bangaren. Yace da ace Najeriya ta dauki darasi daga cutar Ebola da sauran cutukan da suka faru a baya da ba haka ba. Yace idan ka duba zaka ga akwai guraren bada agajon lafiya matakin farko kusa Dubu 10 a fadin kasarnan amma duk basa aiki yanda ya kamata wasu ma kwata-kwata basa aiki.   Ya jawo hankalin kwamitin da cewa su duba yanda ake gudanar da ayyukan lafiya a kasarnan a binciken da zasu yi.
Yawancin abubuwan wanke hannu ba masu kyau bane>>Gwamnatin tarayya

Yawancin abubuwan wanke hannu ba masu kyau bane>>Gwamnatin tarayya

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa yawancin abubuwan wanke hannu dan neman kariya daga cutar Coronavirus ba masu kyau bane.   Shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 kuma sakataren gwamnatin tarayya,  Boss Mustapha ne ya bayyana haka inda yace binciken da suka yi ne ya nuna musu cewa kaso 63 na abin wanke hannun da ake amfani dashi a Abuja ba me kyau bane saboda bashi da rijista da gwamnati. Saida yace hakan ba a Najeriya kadai yake faruwa ba, abune dake Damun Duniya baki daya.   Ya jawo hankalin masu samar da abin tsaftace dasu rika yin me inganci ta yanda ba zai zama wata matsala ba.  
Ku daina wani bugun kirji mara Amfani, ku gayawa membobinku su kiyaye dokokin Coronavirus/COVID-19 saboda kamar yanda ta durkusar da manyan kasashen Duniya, muma da wuya mu tsallake>>Gwamati ta gargadi coci-coci

Ku daina wani bugun kirji mara Amfani, ku gayawa membobinku su kiyaye dokokin Coronavirus/COVID-19 saboda kamar yanda ta durkusar da manyan kasashen Duniya, muma da wuya mu tsallake>>Gwamati ta gargadi coci-coci

Kiwon Lafiya
Sakatafen Gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19,  Boss Mustapha ya gargadi coci-coci da cewa su daina wani bugun kirji mara amfani su gayawa Membobinsu su kiyaye dokokin hana yaduwar cutar Coronavirus/COVID-19.   Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi ta coci-coci daban-daban da aka tara a waje daya inda yace cutar fa ta durkusar da kasashen da suka shafe shekaru 300 sun Dimokradiyya dan haka ba lallai Najeriya itama ta tsira ba. Ya kara da cewa cutar bata da magani a yanzu dan haka kiyaye dokokin da aka ne kawai mafita.
Lokacin sake saka dokar Kulle yayi>>Gwamnatin tarayya

Lokacin sake saka dokar Kulle yayi>>Gwamnatin tarayya

Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa lokaci yayi da zata sake saka dokar kulle saboda yanda cutar Coronavirus/COVID-19 ke kara yawa a kasar.   Sakataren gwamnatin tarayya wanda kuma shine shugaban kwamitin yaki da cutar Coronavirus/COVID-19,  Boss Mustapha ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da manema labarai. Boss Mustapha yace da ace madafan iko a hannunshi suke da tabbas a halin da Najeriya tace ciki yanzu zai sake saka dokar kulle saboda yanda duk da cutar na karuwa amma mutane suna wasa da ita.   Yace yanayin yanda mutane ke rayuwa yanzu sun daina bin dokokin dakile cutar da gwamnati ta saka kamar ma cutar ta wuce.   Yace a yanzu dai babu wanda zai ce be san da wannan cuta ba saboda a kalla ko da baka ga mutum a zahiri wanda cutar ta kashe ko ta k...
Addu’o’in da kuke mana a wannan wata na Ramadana sun taimaka sosai wajan nasarorin da muka samu a yaki da Coronavirus/COVID-19 >>Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Addu’o’in da kuke mana a wannan wata na Ramadana sun taimaka sosai wajan nasarorin da muka samu a yaki da Coronavirus/COVID-19 >>Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Siyasa
Adda'oin da yan nigeria suka duku fa yine yasa cutar covid-19 batayi kamari a kasarnan ba a cewar sakataran gwamnatin taraiyya, Boss Mustafa . Ya fadi haka ne a  ranar talata, 5 gawatan mayu a majalisar wakilai inda ya ke cewa Addo'in dai sunyi tasiri wajan yaki da cutar a kasar nan. Mustafa, dai shine wanda fadar shugaban kasa ta nada a matsayin shugaban kwamitin yaki da cutar covid-19 a Nigeria. Sakataran gwamnatin tarayyan dai yayi bayanin yadda nigeria ke iya kokari ganin dakile cutar a kasar nan yayi jawabin ne dai a majalisa tare da wasu yan mambobin kwamitin nasa, kamar yanda hutudole ya samo. Ya ce a yayin da Nigeria ke kokarin yaki da cutar to Addu'a ce ta kai mu ga matsayar da muke a yanzu haka. A gaskiya Addu'a ta taka mahimiyar rawa a fanin wanda har...
Gwamnatin tarayya ta dage zaman majalisar Koli sai yanda Hali yayi

Gwamnatin tarayya ta dage zaman majalisar Koli sai yanda Hali yayi

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta dakatar da zaman majalisar koli da ta saba yi duk Mako, a Ranar Laraba.   Gwamnati ta dakatar da zaman majalisar ne saboda fargabar Annobar cutar Coronavirus/COVID-19 data Addabi Duniya, ba'a dai bayyana ranar ci gaba da zaman majalisar ba.   Sakataren gwamnatin tarayya,Boss Mustapha ne ya bayyana haka inda yace zaman majalisar manyan kasa da aka shirya yi Ranar Alhamis me zuwa ma an dakeshi.