
Ecuador ta rike Brazil sun tashi wasa daci 1-1 a gasar Copa America amma duk da haka Brazil ta dare saman teburin Group B na gasar
Kasar Brazil ta gaza yin nasara a wasa karo na farko tun shekarar 2019 da Argentina ta lallasa ta daci 1-0, bayan Ecuador ta rike ta sun tashi wasa daci 1-1 a gasar Copa America.
Brazil ta riga da ta dare saman teburin Group B na gasar ta Copa America wanda hakan yasa ta hutar da manyan yan wasan ta, inda su Gabriel Barbosa, Douglas Luiz na Everton, Fabinho da kuma Douglas Luiz duk suka samu damar fara buga wasan.
Lucas Paqueta shima ya buga wasan yayin da suka yi kewar Neymar kuma canjin yan wasan da Brazil tayi yasa tawagar bata yi kokari sosai ba, duk da cewa sune suka fara cin kwallo guda ta hannun Eder Militao.
Brazil tayi nasara a gabadaya wasanni uku data fara bugawa na gasar amma a jiya bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Angel Mena ya ramawa Ecuador kwallon su...