
Direban da aka kama da laifin kisan kai a Legas nima yayi min fyade>> a cewar wata yarinya
Nice (Andrew) Omininikoron, direban motar hayar da aka kama a Legas kan kisan wata fasinja Oluwabamise Ayankole ya sake fadawa cikin wani laifin.
Inda wata yarinya ta bayyanawa manema labarai na Punch cewa yayi mata fyade a cikin motar tasa a ranar 25 ga watan nuwamba shekarar 2021.
Yarinyar ta bayyana cewa yayi mata fyaden ne a matarsa bayan ta tashi daga kasuwa inda ya tilastata kuma taji haushi sosai.