fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: BUA

Me kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya ware Dala Miliyan 100 dan baiwa mutane Tallafi

Me kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya ware Dala Miliyan 100 dan baiwa mutane Tallafi

Uncategorized
Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu Rabiu ya bayyana cewa kamfaninsa ya ware Dala Miliyan 100 dan baiwa jama'ar Najeriya da Afrika tallafi.   Da yake bayyana fitar da kudin, Abdulsamad ya ce zai baiwa bangaren kiwon Lafiya, Ilimi da habaka abubuwan ci gaban al'umma muhimmanci.   Yace duk shekara zai rika ware Dala Miliyan 50 ga 'yan Najeriya da kuma Dala Miliyan 50 ga sauran kasashen Africa. “Over the years as a corporate, and through the BUA Foundation, we have been actively involved in corporate philanthropy in various sectors – from health, education, community development, water & sanitation, sports, and even more recently, our work on COVID-19.
BUA ya sanar da bayarda tallafin karatu ga dalibai 100 da taransifomomin wutar lantarki 6 ga al’ummomin jihar Edo

BUA ya sanar da bayarda tallafin karatu ga dalibai 100 da taransifomomin wutar lantarki 6 ga al’ummomin jihar Edo

Uncategorized
A matsayin wani bangare na gudummawar da take bayarwa ga cigaban al’ummomin da suka karbi bakuncin ta, kamfanin simintin BUA, daya daga cikin manyan kamfanonin siminti a Afirka ya bayar da gudummawar taransifomomi 6 na 500KVA domin bunkasa samar da wutar lantarki ga al'ummomin Okpella na jihar Edo. Haka kuma, kamfanin ya sanar da bayar da tallafin karatun mutane 100 'yan asalin Okpella tare da samar da motocin sintiri na tsaro ga jami'an tsaro a cikin al'umma. Da yake jawabi game da gudummawar, Injiniya Yusuf Binji, Manajan Darakta kuma Shugaba na kamfanin simintin BUA, ya ce alhakin kamfanin simintin BUA na zamantakewar jama'a wani bangare ne mai muhimmanci na kamfanin kuma sakamakon haka, ya himmatu ga ci gaban al'ummomin da ke karbar bakuncin aiki shi. Game da motocin jami'...
Dalilin da yasa muka budewa Dangote da BUA boda su ci gaba da fitar da kaya>>Gwamnatin tarayya

Dalilin da yasa muka budewa Dangote da BUA boda su ci gaba da fitar da kaya>>Gwamnatin tarayya

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan dalilin da yasa ta bar kamfanonin Dangote, BUA da wani kamfanin Iskar Gas su ci gaba da fitar da kaya zuwa kasashen waje.   Kakakin hukumar Kwastam, DC Joseph Attah ya bayyanawa manema labarai cewa, an bar kamfanonin ne su rika kai kaya zuwa wasu kasashen Africa saboda yanda ake bukatar kayayyakin nasu a wadannan kasashe.   Yace ba zai iya tuna sunan dayan kamfanin ba amma duk dan amfanin kasashen Africa ne aka bari ana fitar da kayan.   Da aka tambayeshi ko za'a kara yawan kamfanonin da aka budewa bodar? Yace bai sani ba dan baya aiki a fadar shugaban kasa.   “The Presidency, in its magnanimity, has approved the exemption of three companies, Dangote Cement, BUA and a gas supply firm from its border closure...
Kamar Dangote, Shima BUA gwamnati ta bashi damar ci gaba da fitar da kaya

Kamar Dangote, Shima BUA gwamnati ta bashi damar ci gaba da fitar da kaya

Siyasa
Rahotanni na bayyana cewa shima kamfanin BUA Mallakin Abdulsamad Rabiu,  ya samu amincewar gwamnatin tarayya ya ci gaba da fitar da kaya zuwa kasashen waje.   A jiya ne dai kamfanin Dangote ya sanar da masu hannun jari a kamfanin cewa zai ci gaba da fitar da kaya zuwa Togo da Nijar. A wata wasika da Sahara Reporters ta gano, Shima mamfanin BUA ya tabbatar da samun wannan amincewa inda zai ci gaba da fitar da kaya kasashen waje.
Kamfanin BUA ya bi sahun Dangote shima zai gina matatar mai a jihar Akwa-Ibom

Kamfanin BUA ya bi sahun Dangote shima zai gina matatar mai a jihar Akwa-Ibom

Kasuwanci
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin BUA ya shiga wata yarjejeniya da kamfanin Axens na kasar Faransa dan gina matatar man fetur.   Matatar man Fetur din za'a kammala ta ne nan da shekarar 2024 kuma zata rika samar da gangar mai 200,000 a kowace rana. Shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ne ya wakilci kamfanin nashi inda ya saka hannu a takardun yarjejeniyar a Faransa sai kuma shugaban kamfanin Axens, Jean Sentenac da shima ya saka hannu a madadin kamfanin nashi.   Za'a gina kamfanin ne a jihar Akwa-Ibom. Najeeiya dai na shigo da kashi 90 na man da take amfani dashi daga kasashen waje. Hutudole ya samo muku daga The Africa Report cewa bankuna da dama ne ke ta godon bada bashi dan ayi wannan aiki. Kuma Abdulsamad Rabiu ya bayyana cewa, aikin zai bada sakamakon...
BUA Ya Bada Motocin Daukan Mararsa Lafiya 3, Da Naira Miliyan 200 Ga Gwamnatin Jihar Adamawa

BUA Ya Bada Motocin Daukan Mararsa Lafiya 3, Da Naira Miliyan 200 Ga Gwamnatin Jihar Adamawa

Uncategorized
Gwamna Ahmadu Fintiri ya samu kyautar Naira miliyan 200 da motocin daukar marasa lafiya guda uku daga kamfanin BUA a matsayin tallafi a yakin da ake yi da annobar coronavirus a jihar Adamawa. Alhaji Abdulsamad Rabiu, wanda tsohon Ministan Lafiya na Kasar, Dakta Idi Hong ya wakilta, ya ce wannan matakin zai taimaka wa jihar don dakile yaduwar cutar ta corona. Dakta Hong ya ce ya zuwa yanzu, kungiyar ta BUA Group Foundation ta kashe kusan Naira biliyan 7 don taimakawa gwamnatoci da kungiyoyin kamfanoni a duk fadin kasar sannan ya jaddada cewa kamfanin zai ci gaba da ba da taimako ga ci gaban bil'adama. Da yake mayar da martani bayan da ya karbo takardun motocin da kuma cek din na Naira miliyan 200, Gwamna Umaru Fintiri ya nuna godiyarsa ga Shugaban kungiyar ta BUA sabo...
BUA zai gina kamfanin Simunti a Adamawa

BUA zai gina kamfanin Simunti a Adamawa

Siyasa
Kamfanin BUA ya bayyana cewa zai gina Kamfanin sumuti a jihar Adamawa. Hakan ya fito daga bakin shugaban kamfanin, Abdulsamad Rabiu yayin da suka kaiwa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ziyarar bang girma.   Abdulsamad yace sun gano akwai albarkatun siminti a kananan hukumomin Guyuk da Lamurde kuma suna shirin kafa kamfani a kananan hukumomin sannan kuma zasu samar da wutar lantarki wadda zata baiwa kamfanin wuta ta kuma baiwa kananan hukumomin 2 suma wutar. Yace kamfanin zai samar da ayyukan kai tsaye da wanda bana kai tsaye ba har Dubu 8. Yace sun yi wannan yunkurine a kokarinsu na ci gaba da samar da amfani da abubuwan da aka sarrafa a cikin gida Najeriya sannan kuma suna bukatar goyon baya  gwamnatin jihar.   A nashi bangaren, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa, ya...
Coronavirus: BUA ya baiwa Legas tallafin motocin daukar mara lafiya 5 da Miliyan Dari 2

Coronavirus: BUA ya baiwa Legas tallafin motocin daukar mara lafiya 5 da Miliyan Dari 2

Siyasa
Kamfanin BUA wanda attajirin dan kasuwa, Abdulsamad Rabiu ke shugabanta ya baiwa jihar Legas wadda itace ta fi kowace jiha yawan masu cutar Coronavirus/COVID-19 tallafin motocin daukar marasa lafiya 5 da tallafin kudi,Naira Miliyan Dari 2.   Da yake mika tallafin ga wakilan gwamnatin Legas, Me kula da tsare-tsaren kamfanin,Chimaobi Madukwe ya bayyana cewa suna matukar Alfahari da kasancewa suna aiki da jihar ta Legas inda yace zasu ci gaba da tallafawa a Najeriya wajan yaki da cutar. BUA ya bayar da irin wannan tallafi a jihohin Katsina,Kano da sauransu.
Hotuna: BUA ya baiwa jihar Katsina tallafin Motocin daukar Mara lafiya 3

Hotuna: BUA ya baiwa jihar Katsina tallafin Motocin daukar Mara lafiya 3

Siyasa
Gidauniyar me kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu watau BUA Foundation ta baiwa jihar Katsina tallafin motocin daukar mara lafiya 3.   BUA ya bada tallafin motocinne dan ci gaba da yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar. Gwamnan jihar Katsina,  Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka ta shafinsa na Twitter, kamar yanda hutudole ya samo.   Ya yabawa BUA da wannan kokari inda yace Allah ya saka masa da Alheri.   Saidai yayi amfani da wannan dama inda ya roki BUA din ya tallafa musu a kan ginin gurin killace masu cutar Coronavirus/COVID-19 da jihar ke yi me daukar gadaje 700. https://twitter.com/GovernorMasari/status/1266005983618314240?s=19 A baya dai BUA ya bayar da tallafi me kwari sosai dan tallafawa yaki da cutar Coronavirus/COVID-19 a m...
Shugaban kamfanin BUA ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga jihar Kwara

Shugaban kamfanin BUA ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga jihar Kwara

Kiwon Lafiya
Shugaban Kamfanin BUA, Alhaji Abdulsamad Rabiu ya ba da gudummawar  Naira Miliyan 100 ga asusun bada tallafi kan yaki da cutar Corona na jihar Kwara.     Tallafin yazo ne 'yan makonni bayan da ya bada tallafin biliyan 1 ga wasu jihohin ciki hadda kwara, haka zalika ya bada makamancin wannan tallafin ga gwamnatin tarayya har Naira biliyan 1 tare da karin biliyan 3.3 ga jihohin kano da legas duk dan yaki da cutar Covid-19.   Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Ilorin a ranar Alhamis wacce Babban sakataren yada labarai ya rattaba hannu ga gwamna Abdulrahman Abdulrasaq da mai magana da yawun jihar Covid-19, Mr. Rafiu Ajakaye.   Sanarwar tace a sakamakon tallafin yanzu jihar ta samu jimlar kudi Naira miliyan N230m wanda zai taimaka wajan yaki da cutar. Gw...