
‘Yan Najeriya basu ga komai ba a Mulkin Buhari, kwanannan zasu fara bin bola tsintar abinci>>Buba Galadima
Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Buba Galadima ya bayyana cewa har yanzu 'ya Najeriya basu ga komai ba tukuna a mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ya bayyana hakane a yayin da aka masa magana kan yanda tattalin arzikin Najeriya ya sake shiga karaya. Yace ai nan gaba idan ba'a dauki mataki ba, sai 'yan Najeriya sun fara zuwa bola tsintar abinci.
Yace irin abinda aka yi lokacin Ghana Must Go zai dawo, yace sai kudin kasar sun koma basu da daraja, yanda sai mutum ya kwashi kudade da yawa kamin ya sayi abu kada.
Buba Galadima ya kara da cewa kuma gashi a mulkin shugaban kasar ana ta satar kudi ba kakkautawa. Yace misali gashinan an kama da wani jami'in gwamnatin Buharin da makudan kudade a Dubai amma shiru kake ji ba'a bincikeshiba.
You’...