
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin Sakatarorin 4
SHUGABA MUHmmadu Buhari a ranar Laraba ya rantsar da sabbin sakatarorin din-din-din na Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
Bikin rantsarwar ya gudana ne gab da fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwa na Tarayya, FEC, a zauren taro na Majalisar, da ke Villa, Abuja.
Sabbin Sakatarorin din-din-din su hudu, wadanda suka kunshi maza uku da mace daya, da suka hada da James Sule daga jihar Kaduna sai Ismaila Abubakar daga jihar Kebbi Mista Ibiene Patricia Roberts daga jihar Rivers sai Shehu Aliyu Shinkafi daga Jihar Zamfara.
Wadanda suka halarci taron Majalisar Zartarwar sun hada da Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Man...