
“Ya kamata yan Najeriya su zabi PDP a shekarar 2023 domin ta ceto su daga mawuyacin halin da suke ciki”>> Farfesa Hagher
Shugaban kungiyar dake yiwa Bukola Saraki yakin neman zabe, farfesa Iyorwuese Hagher ya bayyana cewa ya kamata PDP ta tsayar da gwarzon dan siyasa idan har tana so ta doke APC a shekarar 2023.
Ya bayyana hakan ne yayin dayaje Jalingo yakin neman zabe wurin masu hannu da tsaki na jam'iyyar PDP.
Inda ya bayyama cewa duba da halin da Najeriya take ciki yanzu, ya kamata mutane su zabi PDP domin ta ceto su daga mawuyacin halin da suke ciki.
Kuma babu wanda zai iya wannan aikin sai uban gidansa, tsohon shugaban sanatoci Bukola Saraki.