fbpx
Friday, December 2
Shadow

Tag: Bundesliga

Bayern Munich ta koma saman teburin Bundlesliga bayan ta lallasa Dortmund 3-2

Bayern Munich ta koma saman teburin Bundlesliga bayan ta lallasa Dortmund 3-2

Wasanni
Kungiyar zakarun kasar Jamus wato Bayern Munich tayi nasarar lallasa Borussia Dortmund 3-2 a wasan Der Klassiker na farlo na suka buga a wannan kakar. Munich tayi nasarar cin kwallayen ne ta hannun zakarun tan wasan ta wato David Alaba,Lewandowski da kuma Leory Sane,  yayin da Marco Reus da Erling Braut Haaland suka taimakawa Dortmund da kwallaye biyu a wasan. Tauraron dan wasan Bayern, Kimmich ya bar filin wasan cikin hawaye bayan ya samu rauni a gwiwar shi yayin daya yi kokarin kwace kwallo a hannun Haaland. Sakamakon wasan yasa yanzu Bayern Munich ta koma saman teburin gasar Bundlesliga yayin data wuce RB Leipzig da maki biyu  kuma ta wuce Dortmund da Mali uku.
Dortmund 4-0 Freiburg: Jadon Sancho ya kara rasa wasan Dortmund karo na biyu a jere

Dortmund 4-0 Freiburg: Jadon Sancho ya kara rasa wasan Dortmund karo na biyu a jere

Uncategorized, Wasanni
Tauraron dan wasan Ingila wanda Manchester United take farautar siya a wannan kakar wato Jadon Sancho ya kara rasa wasan Dortmund karo na biyu saboda matsalar numfashi da yake fama da shi. Dan wasan Amurika mai shekaru 17 Giovanni Reyna shine ya mayewa kungiyar gurbin Sancho a wasan kuma yayi kokari sosai tare da Haaland yayin da suka taimakawa Dortmund tayi nasarar cin hudu bayan ta sha kashi a makon daya gabata. Dan wasan kasar Norway Haaland yaci kwallaye biyu a wasan yayin da gabadaya kwlayen shi na wannan shekarar suka kama 17 daga wasanni 18 daya buga na Bundlesliga. Emre Can shima yayi nasarar zira kwallo guda a wasan sai kuma ana gab da tashi Haaland ya taimakawa Felix Passlack ya zira kwallo guda wadda ta kasance ta hudu duk da cewa zakaran kungiyar su Sancho bai buga wasan b...
Bayern Munich ta lallasa Schalke 04 da 8-0 a wasan su na farko a gasar Bundesliga

Bayern Munich ta lallasa Schalke 04 da 8-0 a wasan su na farko a gasar Bundesliga

Wasanni
A wasan farko da suka buga na gasar Bundlesliga ta bana da kungiyar Schalke 04, Bayer Munich tawa kungiyar cin rabani da yaro na 8-0.   Gnabry ne ya fara budewa Munich hanya da cin kwallo ta farko, sai Goretzka yaci ta 2, Lewandowski ya ci kwallo ta 2 inda Gnabry ya kara kwallaye 2 a jere, Mueller, Sane, da Musiala duk sunci kwallaye daya-daya kowanensu. Jamal Musiala dan shekaru 17 ya kafa tarihin zama dan kwallo mafi karancin shekatu da ya ciwa Munich din kwallo.   Wannan nasara dai Alamace dake Nuna Munich din ba da wasa suka dawo wannan kakar ba.
Lewandowski ya lashe zaben zakaran dan wasan Bundlesliga na wannan kakar

Lewandowski ya lashe zaben zakaran dan wasan Bundlesliga na wannan kakar

Wasanni
Sama da kashi 50 bisa dari na zaben da aka yi wurin zabar zakaran dan wasan Bundlesliga a wannan kakar tauraron daya fi cin kwallaye masu yawa a gasar suka zaba, wato Lewandowski  a wata sanarwa da hukumar gasar tayi ranar sati. Lewandowski yayi kokari sosai a wannan kakar wasan kuma yaci zaben zakaran dan wasa watan augusta, yayin da kuma yaci gaba da kasancewa dan wasan daya fi cin kwallaye masu yawa a gasar. Dan wasan mai shekaru 31 ya kafa sababbin tarihi da dama a wannan kakar,  yayin daya zamo dan wasa na farko daya ci wasanni guda 11 a jere na gasar Bundlesliga, kuma dan wasan yaci kwallo a gabadaya kungiyoyin gasar Bundlesligan. Lewandowski ya taimakawa Munich wurin lashe kofin gasar karo na takwas a jere. Sauran yan wasan da aka zaba sun hada da Jadon Sancho, Kai H...
Munich 1-0 Bremen: Kwallon Lewandowski tasa Bayern Munich sun lashe kofin gasar Bundlesliga karo na takwas a jere

Munich 1-0 Bremen: Kwallon Lewandowski tasa Bayern Munich sun lashe kofin gasar Bundlesliga karo na takwas a jere

Wasanni
A yau ranar talata Bayern Munich suka yi nasarar lashe kofin gasar Bundlesliga karo na 8 a jere yayin da kwallon da Robert Lewandowski yaci kafin aje hutun rabin lokaci tasa suka tashi 1-0 tsakanin su da Bremen. Kafin a buga wannan wasan, Bayern Munich sune a sama teburin gasar yayin da suka wuce Dortmund da maki bakwai wanda su har yanzu suna da sauran wasanni uku da basu buga ba. Amma yanzu nasarar da suka yi tasa sun kere masu da mako goma. Wannan shine karo na 30 da Bayern Munich suka lashe kofin babbar gasar ta kasar Jamus, kuma har yanzu suna kan bakar su ta lashe kofunan gasa har guda uku. Munich sun buga wasan karshe na gasar kofin Jamus tsakanin su da Leverkusen a ranar 4 ga watan yuli, kuma sunyi nasarar cin Chelsea 3-0 a wasan farko na gasar Champions lig. Robert ...
Borussia Dortmund 1-0 Hertha Berlin: Emre Can ya taimakawa Dortmund a wasan da suka buga jiya

Borussia Dortmund 1-0 Hertha Berlin: Emre Can ya taimakawa Dortmund a wasan da suka buga jiya

Uncategorized
Borussia Dortmund sun cigaba da fafatawa domin suga sun kerewa abokan hamayyar su wato Bayern Munich wanda sune a saman teburin gasar Bundlesliga a yanzu yayin da suka wuce Dortmund da maki bakwai. A jiya Dortmund suka buga wasa tsakanin su da Hertha Berlin kuma sun yi nasarar jefa kwallo guda a wasan, yayin su kuma abokan hamayyar su Munich suka yi nasarar tashi a 4-2 tsakanin su da Leverkusen duk dai a jiyan. Dortmund sun barar da kwallaye dama yayin da tauraron Ingila Jadon Sancho shima ya barar da kwallaye biyu masu kyau, daga bisani kuma Emre Can yayi nasarar cin kwallon daya bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Yayin da aka kusa gama wasan, gabadaya yan wasan Dortmund dana Hertha Berlin guda 22 sun tsugunna a tsakiyar filin wasan sun yi zanga zangar mutuwar wani baki...
Florian Wirtz ya zamo matashin dan wasa mafi karancin shekaru daya zira kwallo a gasar Bundlesliga

Florian Wirtz ya zamo matashin dan wasa mafi karancin shekaru daya zira kwallo a gasar Bundlesliga

Wasanni
Florian Wirtz ya karya tarihin da Nuri Sahin ya kafa a gasar Bundlesliga wanda yaci kallo yana dan shekaru 17 da kwanaki 84 a shekara ta 2005, a wasan da suka buga jiya wanda Munich suka ci su 4-2. Wirtz ya shigo wasan ne bayan an dawo daga hutun rabin lokaci kuma wannan shine wasan shi na hudu, yayi kafa sabon tarihi a kungiyar yayin daya samu damar yin wasa a tawagar yan wasa 11 na farko yana mai shekaru 17 da kwanaki 16. Wirtz yaci kwallon da ba zai taba mantawa da itaba. Wirtz ya wuce dan wasan wasan baya na Munich Lucas Hernandez kafin ya bugawa babban golan jamus da Bayern Manuel Neuer kwallon da kafar shi ta hagu kuma wannan abun kunya ne ga kungiyar Munich. Kochin Leverkusen Peter Bosz Sung ya yaba dan wasan sosai yayin daya ke cewa, Wirtz yana da matukar muhimmanc...
Bayern Munich sun yi nasara a wasan da suka buga da Bayer Leverkusen a yau yayin da suka tashi 4-2

Bayern Munich sun yi nasara a wasan da suka buga da Bayer Leverkusen a yau yayin da suka tashi 4-2

Uncategorized
Bayern Munich sun kara matsawa kusa da lashe kofin gasar Bundlesliga karo na 8 a jere yayin da suka yi nasarar jefa kwallaye har guda hudu a wasan da suka buga tsakanin su da Bayer Leverkusen a yau ranar sati 6 ga watan yuni. Leverkusen sun firgita Munich daga farko yayin da Lucas Alario ya jefa kwallo cikin minti goma na farko a wasan kafin su ci kwallayen su guda hudu, sun ci kwallaye uku kafin a aje hutun rabin lokaci yayin da dan wasan Leverkusen mai shekaru 17 Wirtz yace kwallo ta karshe a wasan. Kingsley Coman, Leon Goretzaka, Serge Gnabry da Robert Lewandowski sune suka ci kwallayen kungiyar Munich yayain da Lucas Alario da Florian Wirtz suka jefa kwallayen Leverkusen. Yanzu Munich sun wuce Dortmund da maki goma. Yan wasan gaba na kungiyar Bayern Munich sun yi kokari ...
Jadon Sancho ya kafa tarihi a kwallon kafa ta kasar Ingila da gasar Bundesliga yayin daya ci kwallaye uku (Hat trick)

Jadon Sancho ya kafa tarihi a kwallon kafa ta kasar Ingila da gasar Bundesliga yayin daya ci kwallaye uku (Hat trick)

Wasanni
A jiya 31 ga watan mayu Jadon Sancho yayi nasarar kafa tarihi a kwallon kafa ta kasar Ingila da kuma gasar Bundesliga yayin daya ci kwallaye har uku a wasan su da Paderburn wanda suka tashi 6-1. Sancho ya bayyana wata riga wadda aka rubuta " a yiwa George Floyd adalci " yayin daya jefa kwallon shi ta farko bayan Thorgan Hazard ya jefa tashi kwallon. Jadon ya jefa kwallon shi ta biyu a minti na 74 yayin da kuma ya jefa kwallon shi ta uku gab da za'a tashi wasan. Yanzu kwallayen Sancho sun kai 15 a wannan kakar wasan, yayin daya zamo dan wasan ingila na farko daya cin kwallaye 15 kuma ya taimaka wurin cin kwallaye guda 15 a kakar wasa guda cikin manyan gasar nahiyar turai guda biyar, tun lokacin da Matt Le Tissier yayi hakan a kungiyar Southampton ta Premier lig shekara ta 1994-95....
Dortmund 6-1 Paderburn: Dortmund sun yi nasara a wasan da suka buga da Paderburn yayin da Sancho yayi nasarar jefa kwallaye har guda uku

Dortmund 6-1 Paderburn: Dortmund sun yi nasara a wasan da suka buga da Paderburn yayin da Sancho yayi nasarar jefa kwallaye har guda uku

Uncategorized
A ranar lahadi 31 ga watan mayu kungiyar Dortmund suka Kara da Paderburn kuma sunyi nasara a wasa  yayin da suka tashi 6-1, kuma Sancho yayi nasarar jefa kwallaye har guda uku a wasan. Gabadaya kungiyoyin basu ci kwallo ba kafin aje hutun rabin lokaci, bayan an dawo kuma da Hazard shine ya fara cin kwallo bayan minti uku Sancho shima ya jefa kwallo daya. Dan wasan ingilan ya bayyana wata riga wadda aka rubuta "a yiwa George Floyd adalci bayan yaci kwallo shi ta farko a wasan. Dortmund sun sha gwagwarmaya kafin aje hutun rabin lokaci yayin da tauraron su Haaland bai buga wasan ba saboda yana da rauni. Bayan Dortmund sun ci kwallo biyu, dan wasan Paderburn Hunemeier yaci kwallo daya kuma bayan minti biyu Sancho ya kara cin wata cin wata kwallon. Yayin da aka kusa gama wasan Ac...