
Gwamnati zata saka ranar Kulle Asusun Bankunan wanda basu hada NIN dinsu da Asusunsu ba
Ministan Sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami ya bayyana cewa nan ba da Jimawa ba gwamnatin tarayya zata saka ranar kulle Asusun wanda basu hana lambar NIN da Asusun nasu ba.
Ya bayyana hakane bayan zaman majalisar Zartaswa. Tuni dai dama Ministan ya bayyana cewa, za'a maye gurbin BVN da NIN.