fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Calaba

‘Yan sanda sun cafke mutum uku da ake zargi da lafin garkuwa da mutane a jihar Calabar

‘Yan sanda sun cafke mutum uku da ake zargi da lafin garkuwa da mutane a jihar Calabar

Tsaro
Rundunar ‘yan sandan jihar  Kuros Riba ta ceto wani mutum da a kai garkuwa da shi, mai suna Emmanuel Akpan-Udo, yayin da aka cafke mutum uku wadanda ake zargi da yin garkuwa da shi. A wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Abdulkadir Jimoh, wanda a ka rabawa manema labarai a  ranar Lahadi, ta ce an cafke wadanda ake zargin ne a ranar 21 ga watan Nuwamba a Calabar. Hakanan Sanarwar ta ce, an kuma samu nasarar kwato motar wadanda lamarin ya rutsa da su a yayin aikin da jami’an su gudnar a Calabar. Wadanda ake zargin sun hada da Etim-Sunday, Mai shekaru 33, Samuel Udo-Udo, mai shekaru 27, da Ime John-Effiong, mai shekaru 23.