
Bidiyo: Matasa a Calabar sun dakawa gidajen ‘yan siyasa wawa da Konasu
Bayan fasa rumbun ajiyar kayan tallafin Coronavirus/COVID-19 suka wawushe a jiya, Juma'a, matasa sun kuma fasa wasu shaguna da gidajen 'yan siyasa a a Calabar, Cross-River.
Lamarin ya dauki kamari sosai da safiyar yau, Asabar inda aka ga matasan sun je gidan dan siyasa dake wakiltar jihar a majalisar dattijai suka kwashi abinda zasu kwasa sannan suka konashi.
https://twitter.com/ogundamisi/status/1319935292686635008?s=19
Vanguard tace matasan sun kona ofishin kungiyar kwadago ta, NLC, da ofishin INEC, da wasu manya filazoji a jihar.