
Wani Direban Motar haya ya mika Fasinjansa zuwa Ofishin ‘yan sanda sakamakon kin sanya takun-kumin Hanci
Wani Direban tasi a kasar Canada ya mika wani fasinjansa zuwa gun 'yan sanda a sakamakon kin sanya takun-kumin kariya na cutar mai sarke Numfashi wato coronavirus.
Rahotanni sun nuna cewa, tun da fari Fasinjan yaki yin biyayya da kin sanya takun-kumin wanda ta kai har hannun sa ya taba fuskar Diraban kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Hakan ne ya fusata Direban motar inda nan take ya kira numbar ofishin 'yan sanda inda ya shaida musu abin da ke faruwa, daga bisani ya rankaya da mutumin zuwa ga Ofishin jami'an wanda anan ne ido ya raina fata, Ai kuwa tuni jami'an 'yan sandan suka cika hannu da mutumin Wanda a karshe a kaci Tatar sa harkimanin Dala $230.