
Shugabannin Kudu-Maso Kudu sun Nemi a sake fasalin Najeriya
Gwamnoni da mutanen yankin Kudu maso Kudu sun nemi a sake fasalin Najeriya, bisa tsarin na gaskiya don tabbatar da zaman lafiya, tsaro, da kwanciyar hankali na kasa.
Shugabannin Kudu-maso-Kudu da tawaga daga fadar shugaban kasa sun halarci wan taro a gidan Gwamnati da ke Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas a ranar 24 ga Nuwamba, 2020, inda a nan ne suka gabatar da wannan kudurin nasu.
Shugabannin Kudu maso Kudu sun yi imanin cewa babu zaman lafiya a kasarnan kuma kasarnan ba ta aiki yadda ya kamata, musamman ga mutanen yankin.