
Yan wasan Real Madrid guda biyu Eden Hazard da Casemiro sun kamu da cutar Covid-19
Real Madrid ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa yan wasanta guda biyu Eden Hazard da Casemiro sun kamu da cutar korona a gwajin da aka yiwa yan wasa da ma'aikatan kungiyar jiya ranar juma'a.
Kungiyar ta kara da cewa gabadaya sauran yan wasanta da kuma ma'aikatan na tawagar farko basu kamu da cutar ba yayin da su kuma Hazard da Casemiro zasu cigaba da killace kansu.
Casemiro da Hazard sun kamu da cutar ne bayan abokin aikin su Militao ya kamu da cutar a makon daya gabata kuma yanzu yan wasan ba zasu buga wasan da Real zata kara da Valencia ba a gasar La Liga.
Sanna kuma yan wasan ba zasu yi tafiya izuwa kasashen suba domin buga wasanni a hutun da za'a bayar na buga wasannin kasashe amma zasu fara bugawa Madrid wasa bayan an dawo daga hutun.
Real Madrid have announ...