fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: CBN

Mun baka awanni 72 ka bayyana gaban mu dan bayani kan batan Dala Miliyan 9.5>>Majalisa ga shugaban CBN

Mun baka awanni 72 ka bayyana gaban mu dan bayani kan batan Dala Miliyan 9.5>>Majalisa ga shugaban CBN

Siyasa
Majalisar Dattijai a karkashin kwamitin dake kula da yanda ake kashe kudin gwamnati ya baiwa shugaban babban bankin Najeriya,CBN, Godwin Emefiele awanni 72 ya bayyana a gabansa dan jawabi kan yanda Dala Biliyan 9.5 ta bace.   Kudin dai na ruwa ne da suka taru akan kudin harajin man fetur da aka tara. Shugaban Kwamitin, Matthew Urhoghide ya bayyana cewa an kwashe kudinne a Asirce daga Asusun.   Majalisar tace akwai abubuwa da yawa da ya kamata shugaban babban bankin yayi jawabi akansu.  
Wasu manyan kasashen Duniya na son wargaza Najeriya>>Obadiah Mailafiya

Wasu manyan kasashen Duniya na son wargaza Najeriya>>Obadiah Mailafiya

Uncategorized
Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya,  CBN, Obadiah Mailafiya ya  bayyana cewa wasu manyan kasashen Duniya na son wargaza Najeriya.   Ya bayyana hakane yayin da yake magana akan matsalar tsaro a mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda yace Ko kusa ba za'a hada zamanin Abacha da na Buhari ba, idan da Abacha ne da ba zai amince da wannan abinda ke faruwa ba.   Yace Turawan yamma sun hurewa wasu mutane kunne inda suka gaya musu cewa dole sune zasu mulki kasarnan, kuma suka basu makamai.  Yace sun shiga daji sunawa mutane kisan kare dangi. A former Deputy Governor of the Central Bank of Nigeria, Dr. Obadiah Mailafia, Wednesday accused world powers of trying to destroy the country. In today’s international system, the four great powers according t...
CBN ya rage harajin da ake biya idan mutum ya aika da kudi ta sakon waya

CBN ya rage harajin da ake biya idan mutum ya aika da kudi ta sakon waya

Kasuwanci
Babban bankin Najeriya da ma'aikatar sadarwar kasar sun bullo da sabon tsarin haraji kan masu mu'amalar da ta shafi yin amfani da wayar salula wajen aikawa da kudi ko sayen katin waya ko 'data'. Bankin ya ce daga wannan Talatar, za ake cire harajin N6.98 kan kowanne kati ko 'data' da aka saye na layin waya ko kuma aikawa da kudi. A baya ana cire N20 zuwa sama kan kowacce mmu'amala da ta shafi aikawa da kudi ko sayen katin waya ko 'data' ta wayar salula. Ya ce sabon tsarin na cikin yarjejeniyar da aka cimma da bankuna da kamfanonin sadarwa bayan wata tattaunawa a jiya Litinin kan bashin naira biliyan 42 da ake bin kamfanonin sadarwa. Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa haɗin-gwiwa da aka fitar tsakanin babban bankin da kamfanonin sadarwar. Wannan tsari dai zai soma aiki ne da...
Babban Bankin Najeriya, CBN Ya Bada rancen Biliyan N4 Ga Noman Shinkafa a Jigawa

Babban Bankin Najeriya, CBN Ya Bada rancen Biliyan N4 Ga Noman Shinkafa a Jigawa

Kasuwanci
Babban bankin Najeriya (CBN) ya raba naira biliyan 4 a matsayin rance ga manoman shinkafa a jihar Jigawa. Biyan kudin yana karkashin shirin Anchor Borrower’s na gwamnatin tarayya. Kodinetan shirin a jihar, Abdu Ahmadu, yayin da yake jawabi a lokacin rabon kayayyakin noman rani na 2021 ga mambobin kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya, (RIFAN), reshen jihar Jigawa ya ce shirin na da nufin taimakawa kananan manoma a kasar. Ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin jihar ta mayar da sama da naira miliyan 700 ga bankin koli, biyo bayan wadataccen abinci na alkama ga manoma a karkashin shirin a jihar. Don haka, ya nemi goyon bayan ma'aikatu da hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki a jihar da su hada kai da bankin. Wakilin RIFAN a jihar, Auwal Mu...
Majalisa ta gayyaci Gwamnan CBN dan jin ba’asin da yasa aka dakatar da hadahadar Cryptocurrency

Majalisa ta gayyaci Gwamnan CBN dan jin ba’asin da yasa aka dakatar da hadahadar Cryptocurrency

Kasuwanci
Majalisar dattijai ta nemi gwamnan babban bankin Najeriya,  CBN, Godwin Emefiele da kuma daraktan SEC, Lamido Yuguda da su gurfana a gabanta dan ba'asin dalilin dakatar da hadahadar kudaden Internet,  Cryptocurrency.   Sanata istifanus Gyang da Tokunbo Abiru ne suka kai kudirin gaban majalisar inda kuma majalisar ta amince da gayyatar wadannan shuwagabannin.   Majalisar ta neki Kwamitin dake kulda da tsaron yanar gizo dana kudi dana kimiyya da fasaha su zauna da Gwamnan CBN da Daraktan SEC su samar da Rahoto akan lamarin.
Ana amfani da kudin Internet na Cryptocurrency wajan karfafawa ta’addanci>>CBN

Ana amfani da kudin Internet na Cryptocurrency wajan karfafawa ta’addanci>>CBN

Kasuwanci
Babban bankin Najeriya,  CBN ya kare dakatar da hadahadar kudaden kudin Internet na Cryptocurrency da yayi.   A sanarwar da daraktan sadarwar CBN, Osita Nwosinobi ya fitar, ya bayyana cewa kudin na Cryptocurrency ba'a san masu amfani dasu ba, watau ana amfani dasu ne ba tare da tantance su wanene ke hadahada da su ba.   Yace hakan yana taimakawa wajan amfani da kudi  a sayi kwaya da kuma safarar kananan makamai, da kuma taimakawa ta'addanci. Hutudole ya fahimci cewa, sanarwar ta kara da cewa wannan dakatarwar a cewar CBN ba zata hana kamfanonin kimiyya da fasaha ci gaba ba a Najeriya, kamar yanda Dailytrust ta ruwaito. “The use of cryptocurrencies in Nigeria are a direct contravention of existing law. It is also important to highlight that there is a critical d...
Kungiyoyin matasan Arewa dana kudu sun goyi bayan hana hadahadar kudin Intanet, Cryptocurrency da CBN yayi

Kungiyoyin matasan Arewa dana kudu sun goyi bayan hana hadahadar kudin Intanet, Cryptocurrency da CBN yayi

Uncategorized
Kungiyoyin matsan Arewa na, ACYM, dana Inyamurai dana Yarbawa dana jihohin tsakiyar Najeriya gaba daya sun hada baki inda suka amince da dakatar da hadahadar kudin Internet, Cryptocurrency da babban bankin Najeriya, CBN yayi.   Kungiyoyin sun fitar da sanarwar hadaka wadda suka ce CBN yayi abin yabo.   Hutudole.com ya ruwaito muku cewa, sun karfafa CBN da cewa kada yayi kasa a gwiwa wajan habaka ayyukan banki dama tattalin arzikin Najeriya. ”We know of a fact that this policy is a hard hit against financial criminals of the underworld who in turn will stop at nothing in their desperate bid to ensure that the policy is changed so that they can continue to have their way. We urge the CBN team not to succumb to any pressure. The policy should be strictly implement...
Kwamitin majalisan wakilai ta gayyaci NNPC da CBN kan zargin bacewar tiriliyan N3.2 na kudin mai

Kwamitin majalisan wakilai ta gayyaci NNPC da CBN kan zargin bacewar tiriliyan N3.2 na kudin mai

Siyasa
Majalisar wakilai ta gayyaci Babban Manajan Darakta na Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mista Mele Kyari, da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele kan zargin rashin shigar da kudaden shiga na Naira tiriliyan 3 da biliyan 235 (dala biliyan 19.253) da aka samu daga sayar da danyen mai na cikin gida a shekarar 2014. Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin asusun, Mista Wole Oke, ya bayar da wannan umarnin a yayin sauraren binciken binciken da aka yi game da tambayoyin binciken da ofishin Odita Janar na Tarayya (AuGF) ya bayar na lokacin da ake dubawa. Sammacin ya zo ne kwanaki 10 kacal bayan da shugaban kamfanin na NNPC ya ki mutunta goron gayyatar da aka aike masa a makon da ya gabata, kan zargin cire dala biliyan 20.301 ba bisa ka’ida ba daga asusun rarar man fetu...
Mutanen Jihar Benue zasu yi zanga-zanga saboda kin basu bashin NIRSAL/CBN duk da cewa sun cika kowane sharadi

Mutanen Jihar Benue zasu yi zanga-zanga saboda kin basu bashin NIRSAL/CBN duk da cewa sun cika kowane sharadi

Siyasa
Wasu mutane a jihar Benue su kimanin 5000 da suka nemi bashin gwamnati karkashin NIRSAL/CBN sun bayyana cewa, zasu yi zanga-zanga idan ba'a basu bashin ba.   Sun bayyana hakane a wata ganawa da suka yi da manema labarai a Makuridi inda shugabansu, Fasto James Shakaa ya bayyana cewa sun baiwa gwamnatin nan da zuwa karshen watan Disamba idan basu ji wani Labari ba to zasu yi zanga-zanga.   Yace sun cike duk wani sharadi da aka bukacesu tun shekarar 2014 amma har yanzu ba'a basu kudin ba amma wasu da suka cike bashin kwanannan an basu bashin ta wata hanya me cike da alamar tambaya.   Yace idan da an bayar da bashin yanda ya kamata da ya taimakawa harkar noma sosai. Amma hakan bata samu ba kamar yanda. TheNation ta ruwaito.   Kokarin jin ta bakin Wak...