
Real Madrid ta dare saman teburin gasar La Liga bayan ta lallasa Celta Vigo daci 2-0
Kungiyar Celta Vigo ta kasance tana sumun nasara a wasannin ta tun ranar 21 ga watan nuwamba amma Real Madrid ta kawo karsen wannan nasarar data samu bayan Asensio ya taimakawa Lucaz Vasquez ya zira kwallon a cikin
mintina shida kacal da fara wasa.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Asensio yayi nasarar cin tashi kwallon da taimakon Casemiro wadda tasa aka tashi Madrid na cin 2-0 kuma ta lashe gabadaya makin wasan.
Sakamakon wasan yasa yanzu Real Madrid ya dare saman teburin gasar La Liga sa maki 36 yayin da wuce Aetico Madrid da maki guda a saman teburin gasar.