fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Tag: Chadi

Gwamnatin tarayya ta fara neman goyon baya daga kasar Chadi dan kawo karshen Boko Haram

Gwamnatin tarayya ta fara neman goyon baya daga kasar Chadi dan kawo karshen Boko Haram

Tsaro
Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ya umarci sojoji a kan ayyuka daban-daban da su fara wani shiri game da masu aikata laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar kasa da tsaro. Ya kuma ayyana shekarar 2021 a matsayin shekarar da tayar da kayar baya za ta kare a kasar. Ministan ya ba da wannan umarnin ne lokacin da Jakadan Chadi a Najeriya, Abakar Chachaimi, ya ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja. Wannan ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis ta hannun mai taimaka wa ministar kan harkokin yada labarai, Mohammad Abdulkadri, mai taken, ‘Rashin tsaro: Ministan Tsaro ya ayyana shekarar 2021 ta yanke hukunci kan kawo karshen tayar da kayar baya’. Magashi ya fadawa Jakadan na Chadi cewa, “Yanzu lokaci ne da shekara don hada karfi da hadin...
Najeriya zata fara baiwa kasar Chadi wutar lantarki

Najeriya zata fara baiwa kasar Chadi wutar lantarki

Siyasa
Najeriya zata fara baiwa kasar Chadi wutar lantarki, kamar yanda kamfanin kula da wutar Lantarki na kasa, TCN ya bayyana.   TCN ya bayyana cewa a makon da ya gabata yayi ganawa da wakilan kasar Chadi Wanda suka zowa Najeriya da wannan buka kuma suma duba ta da yiyuwar Amincewa. A yanzu haka dai Najeriya na baiwa kasashen Nijar, Togo da Benin wutar Lantarki.   “Meeting between Ministry of Power, TCN, and the Chadian Minister of Energy, Mrs Ramatou Mahamat Houtouin, to discuss the possibilities of connecting the Republic of Chad to the Nigerian national grid [was held] on Wednesday, October 21, 2020,” the TCN said on its Twitter handle on Sunday, alongside pictures of the meeting.
Dakarun MJTF dake kasar Chadi sun ceto Mata da yara 8 daga hannun ‘yan ta’adda

Dakarun MJTF dake kasar Chadi sun ceto Mata da yara 8 daga hannun ‘yan ta’adda

Tsaro
Sojoji dake sashi na 2 na (Multinational Joint Task Force (MJTF) a Jamhuriyar Chadi sun ceto mutane 12, ciki har da yara takwas, da ke hannun 'yan ta'addan Boko Haram (ISWAP), bayan sun yi kwanton-bauna kan maharan a kusa da Barkalam, dake yankin  Tafkin Chadi kusa da kan iyakar Najeriya. A yayin samamen kwale-kwale uku na ‘yan ta’addan sun kife, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kame wasu mayakan na ISWAP tare da jikkata wasu, a cewar Kanar Mohammed Dole, kakakin MJTF, a  wata sanarwa da ya fitar. A cewar sa, babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Chadi (CDS), Laftanar Janar Abakar Abdelkarim shine ya karbi mutanen da aka kubutar a sansanin sojin, inda ya sha al'washin cigaba da jajircewa kan yaki da 'yan ta'addan.      
Sojojin kasar Chadi sun kashe Boko Haram 20

Sojojin kasar Chadi sun kashe Boko Haram 20

Tsaro
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa sojojin kasar sun kashe mayakan Boko Haram 20 a kamar yanda sanarwar data fito daga kasar jiya, Juma'a ta bayyana, inda kuma suka kubutar da mutane 12 da kungiyar ta yi garkuwa dasu.   Boko Haram ranar 17 ga watan Satumba ta sace wasu mutane, inda sojoji suka bisu suka kashe 15 daga ciki tare da kubutar da mutanen da suka sace din, kamar yanda majiyar gwamnati ta gayawa AFP. Hakanan sojojin Chadin sun sake yin Artabu da Boko Haram din a garin Bilabrim inda suka kashe 5, sojoji 2 suka jikkata.
Kasar Chadi ta roka Najeriya da ta samar mata da wutar lantarki

Kasar Chadi ta roka Najeriya da ta samar mata da wutar lantarki

Siyasa
Gwamnatin kasar Chadi ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta hada kasar da tsarin wutar lantarkin Najeriya. Jakadan Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chachaimi ne ya gabatar da wannan bukata yayin ziyarar aiki da yakawo ma ministan wutan lantarki. Yayin da yake bayyana bukatar shi, jakadan ya jaddada muhimmin tarihi da tattalin arziki na hada Chadi da wutar lantarki a Najeriya a matsayin wata hanya ta ci gaba da hadin gwiwa tsakanin kasashen. Da yake amsa tambaya, Engr. Mamman ya yi maraba da wannan ci gaba, yana mai jaddada cewa, zai taimaka wajen inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Ministan ya ce bukatar daga Jamhuriyar Chadi ta zo a lokacin da ya fi dacewa yayin da yake tabbatar wa wakilin Chadi cewa Najeriya za ta kimanta hakan a cikin ayyukan da ake yi a karka...
Majalisar dokokin Chadi ta soke hukuncin kisa kan ‘yan ta’adda

Majalisar dokokin Chadi ta soke hukuncin kisa kan ‘yan ta’adda

Tsaro
Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da wata doka da ta hana aiwatar da hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da aikata laifuffukan da suka shafi ta’addanci.     Ministan shari’ar kasar Djimet Arabi ya sanar da dfaukar matakin, shekaru 4 bayan Chadi ta jingine aiwatar da hukuncin kisa kan kowanne laifi.     Arabi wanda ya gabatar wa majalisar dokoki da kudirin yace 'yan majalisun sun amince da dokar ba tare da hamayya ba.     Ministan yace matakin wani yunkuri ne na samar da dokar bai daya kamar yadda kasashen yankin Sahel suka yi, kuma dokar zata fara aiki da zarar shugaba Idris Deby ya rattaba hannu akan ta.
Hotuna:Kalli yanda ‘yan majalisar kasar Chadi suka kaiwa shugaban kasarsu ziyarar Goyon baya a Sabon  mazauninshi dake Daji

Hotuna:Kalli yanda ‘yan majalisar kasar Chadi suka kaiwa shugaban kasarsu ziyarar Goyon baya a Sabon mazauninshi dake Daji

Siyasa
Shugaban kasar Chadi,Idris Derby ya sha Alwashin ganin karshen Boko Haram a kasarsa, wanda hakanne yasa ya shiga gaba wajan jagorantar sojojinshi zuwa Yakar Kungiyar.   Shugaban ya kafa Fada ta wucin gadi a cikin Dajin inda yake duba yanda Sojojin nashi ke fatattakar Boko Haram.   Wadannan hotunan 'yan Majalisar Kasarne da suka kaiwa shugaban ziyara a matsuguninshi dake cikin daji inda suka nuna goyon bayansu gareshi a wannan yunkuri na ganin karshen Boko Haram.   Boko Haram dai ta kashewa kasar Chadi sojoji kusan 100 wanda hakan yasa shugaban kasar yace sai sun dauki fansa.      
Sojojin Kasar Chadi da suka yi fata-fata da Boko Haram sun kwato sojojin Najeriya da kungiyar ke garkuwa dasu

Sojojin Kasar Chadi da suka yi fata-fata da Boko Haram sun kwato sojojin Najeriya da kungiyar ke garkuwa dasu

Siyasa
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa sojojin kasar a harin kare dangi da suke ci gaba da kaiwa matsugunan mayakan kungiyar Boko Haram sun kwato wasu sojojin Najeriya da kungoyar ke garkuwa dasu.   Rahoton wanda Daily Post ta ruwaito yace wata majiyace daga yankin ta shaida haka.   Shugaban kasar Chadi,Idris Derby ne da kansa ke jagorantar wannan hari wanda ke zuwa bayan Boko Haram din ta kashe sojojin kasar fiye da 100.   Rahoton yace shugaba Idris Derby na shawagi ta saman yankin Tafkin Chadi a jirgin sama inda yake ganin yanda sojojin nashi ke fatattakar Boko Haram.   Rahoton ya kara da cewa mayakan Boko Haram din sun tsere cikin Najeriya inda aka kama wasu,wasu kuma aka kashesu.   Akwai Rahoton dake cewa, Shugaba Idris Derby ya bayyan...
Hotuna: Yanda Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojin kasarshi suka kaiwa Boko Haram hari

Hotuna: Yanda Shugaban kasar Chadi ya jagoranci sojojin kasarshi suka kaiwa Boko Haram hari

Siyasa
Shugaban kasat Chadi,Idris Derby ya dauki hankula sosai bayan bajintar da yayi ta jagorantar sojojinshi suka kaiwa masu tada kayar baya na Boko Haram Hari.   Rahotanni sun bayyana cewa harin wanda Kasar ta Chadi ita kadsi ta kaishi da manyan makamai na sojojin kasa dana sama ya tarwatsa maboyar 'Yan ISWAP dana Boko Haram inda suka rika gudu suna shigewa cikin Najeriya ba tare da fuskantar kalubale daga bangaren sojojin Najeriya ba. HumAngle ya ruwaito cewa dama tun a baya shugaban na Chadi yace kisan da Boko Haram din tawa sojojinshi kusan 100 ba zai tafi a banza ba tare da ramuwar gayya ba. Mayakan Boko Haram sun shiga garuruwan Magumeri da Gubiyo inda gurine dama me hadarin gaske inda a nanne sukawa sojojin harin kwantan Bauna daya kashe kusan sojin 100 hakanan a...