
Kasar Amurka ta gargadi China kan takurawa Musulmai
A karon farko tun bayan darewa shugabanci a watan jiya, shugaba Biden na Amurka ya yi magana da takwaransa na China Xi Jinping.
Fadar White House ta ce Mista Biden ya nuna damuwa kan fadada ikon Beijing a Hong Kong, tare da gargaɗin shugaban a kan yadda gwamnatinsa ke takurawa musulmin Uighur a jihar Xinjiang.
Sun kuma yi musayar ra'ayi kan canjin yanayi da haɓakar makaman nukiliya.
Dangantaka tsakanin manyan ƙasashe biyu masu ƙarfin tattalin arziki a duniya ta yi tsamin da bata taba yi ba.
Lokaci na karshe da shugaban kasashe Amurka da China suka yi magana kai tsaye shi ne a watan Maris din shekarar da ta gabata.
A bayan bayan nan ne BBC ta samu muhimman shaidu da ke bayyana yadda ake yi wa mata fyade da azabtarwa a sansanonin killace Musulmai ƴa...