fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Tag: Champions League

Covid-19: Za’a buga wasan farko na kusa dana kusa dana karshe tsakanin Madrid da Liverpool na gasar zakarun nahiyar turai a kasar Sifaniya

Covid-19: Za’a buga wasan farko na kusa dana kusa dana karshe tsakanin Madrid da Liverpool na gasar zakarun nahiyar turai a kasar Sifaniya

Wasanni
Za'a buga wasan ne a filin Alfredo Di Stefano na kungiyar Real Madrid Castilla a ranar 6 ga watan afrilu, maimakon a buga shi a aslin filin tana Santiago Bernabeu wanda ake gudanar da gyara a filin yanzu haka. A watan disemba ne kasar Sifaniya ta hana yan Ingila shigar mara kasa saboda barkewar cutar sarkewar numfashi. Amma yanzu kasar Sifaniya ta tabbatar da cewa zata sassauta wanda dokar a ranar 30 ga watan maris wanda hakan zai baiwa kungiyar Liverpool damar shiga kasar domin su buga wasan farko na kusa dana kusa dana karshe a gasar zakaru nahiyar turai tsakanin su da Madrid. Covid-19: Champions League: Liverpool's quarter-final first-leg tie against Real Madrid to go ahead in Spain The match will take place at Real Madrid Castilla's Alfredo Di Stefano ground on Ap...
An zabi kwallon Messi da ya ci a wasan su da PSG a matsayin kwallon mako ta gasar Champions League

An zabi kwallon Messi da ya ci a wasan su da PSG a matsayin kwallon mako ta gasar Champions League

Wasanni
Lionel Messi yayi nasarar cin kyakkyawar kwallo a wasan Barcelona da Paris Saint Germn na gasar zakarun nahiyar turai a makon daya gabata, wadda tasa dan wasan ya samu kyauta. Kwallon Messi ta doke ta De Bruyne wadda yaci a wasan Man City da Monchengladbach, da kuma kwallon nesa da Luis Muriel yaci Real Madrid sai kuma ta Salah wadda yaci a wasan su da RB Leipzig. Ga bideyon kwallon kamar haka: https://twitter.com/FCBarcelona/status/1372951249683951626?s=19 Lionel Messi’s PSG stunner named UCL goal of the week Lionel Messi’s brilliant goal against Paris Saint-Germain has been named the Champions League Goal of the Week. Of course the goal actually happened last week, but nevermind, Messi’s still scooped yet another prize for his brilliant golazo against the ...
Bayern Munich ta cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai sau 19, fiye da kowace kungiya a tarihin gasar

Bayern Munich ta cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai sau 19, fiye da kowace kungiya a tarihin gasar

Wasanni
Kungiyar Bayern Munich ta cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai bayan ta lallasa Lazio daci 2-1 a jiya, inda doke ta daci 6-2 kenan a wasannin gida da waje. Bayern ta lallasa Lazio daci 4-1 a wasan waje da suka fara bugawa a Rome, inda kuma a jiya Robert Lewandowsku yaci mata bugun daga kai sai mai tsaron raga, wadda ta kasance kwallon shi ta 39 a wannan kakar. Kungiyar Jamus din ta kara zira kwallo guda a wasan ta hannun Choupo-Moting wanda ya musanyi Lewandowski kafin Lazio ta rama guda ta hannu Marco Porolo. A karshe dai sakamakon wasan yasa yanzu Bayern Munich ta zamo kungiya ta farko data cancanci buga wasannin kusa dana kusa dana karshe sau 19 a tarihin gasar zakarun nahiyar turai. 19 - Bayern Munich have reached the quarter-fin...
Madrid ta cancanci buga wasan kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai bayan ta lallasa Atalanta daci 4-1 a wasannin gida da waje

Madrid ta cancanci buga wasan kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai bayan ta lallasa Atalanta daci 4-1 a wasannin gida da waje

Wasanni
Karim Benzema yayi nasarar cin kwallo a wasanni biyar a jere yayin da Real Madrid ta cancanci buga wasan kusa dana kusa dana karshe a gasar zakarun nahiyar turai, bayan lallasa Atalanta daci 4-1 a wasannin gida da waje. Kungiyar La Ligan tayi nasarar cin 1-0 a wasan waje da suka fara bugawa a gidan Atalanta, kafin jiya tayi nasarar cin 3-1 a gidan ta inda kuma Atalanta ta barar da damarmaki da dama kafin Madrid ta fara jagoranci ta hannun Benzema. Kaftin din Madrid Sergio Ramos yaci bugun daga kai dai mai tsaron raga kafin daga bisani Luis Muriel ya ciwa Atalanta kwallo guda da bugun nesa, amma a karshe Asensio ya shigo daga benci ya ciwa Real Madrd kwallo ta uku ana daf da tashi wasa. Real Madrid 3-1 Atalanta (agg 4-1): Karim Benzema scores as Real Madrid reach Champions ...
Champions League: Liverpool ta share gwagwarmayar da take sha a Premier League, ta lallasa Leipzig daci 2-0

Champions League: Liverpool ta share gwagwarmayar da take sha a Premier League, ta lallasa Leipzig daci 2-0

Wasanni
Kungiyar Liverpool, wadda ta fadi wasannin gida shida a jere na Premier League ranar lahadi a hannun Fulham ta kai hare hare a wasan tada Leipzig kafin aje hutun rabin lokaci sai dai ta gaza zira kwallon cikin raga. Amma daga bisani bayan an dawo daga hutun ta zira kwallaye biyu cikim mintina hudu ta hannun gwarazan yan wasanta wato Mohammed Salah da kuma Sadio Mane, wanda hakan yasa ta cancanci buga wasannin kusa da karshe na gasar zakarun nahiyar turai. Kuma kwallaye biyu data ci sun sa yanzu ta lallasa RB Leipzig daci 4-0 idan aka hada da wasan farko da suka buga, yayin da kuma wasan ya kasnce na uku da Liverpool taci a cikin wasanni tara da suka gabata. Liverpool put their Premier League struggles behind them as they beat RB Leipzig 2-0 at the Puskas Arena to secure a ...
PSG ta cire Barcelona da ga gasar Champions League:Mbappe ya kafa Tarihi, Za’a Buga wasannin quarter Finals ba tare da Messi da Ronaldo ba tun shekarar 2005

PSG ta cire Barcelona da ga gasar Champions League:Mbappe ya kafa Tarihi, Za’a Buga wasannin quarter Finals ba tare da Messi da Ronaldo ba tun shekarar 2005

Wasanni
Kungiyar Kwallon kafa ta PSG ta cire Barcelona daga gasar Champions League ta bana.   Sun tashi wasan yau da sakamakon kunnen doki wanda a wasan farko kuma da aka yi PSG ce ke da kwallaye 4 a Ragar Barca. Haka yasa Barca ta fita daga gasar.   Messi ya ciwa Barca kwallo amma kuma ya barar da Penalty wadda Navas ya tare. Kylian Mbappe ne ya ciwa PSG kwallonta wanda hakan yasa ya zama dan kwallo na farko a Tarihin Duniya da yaci Barcelona kwallaye 4 a wasan Champion League na kamin a kai na kusa dana karshe.   A karin farko run shekarar 2005 za'a buga wasannin Champions League na kusa dana kusa dana karshe ba tare da taurarin 'yan kwallon Duniya ba, Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.
A karo na farko kungiyoyin gasar Jamus guda hudu sun cancanci buga wasannin karshe na gasar zakarun nahiyar turai, tun kakar 2014/15

A karo na farko kungiyoyin gasar Jamus guda hudu sun cancanci buga wasannin karshe na gasar zakarun nahiyar turai, tun kakar 2014/15

Wasanni
Ta farkon su itace kungiyar zakarun gasar, wato Bayern Munich wadda ta lashe kofin gasar a shekarar data gabadata, sannan kuma a yanzu ta kasance a saman Group A da maki 16 bayan data lallasa Lokomotiv Moscow 2-0 a jiya. Sai kungiyar Borussia Dortmund wadda itama ta kasance a saman Group F na gasar da maki 13 bayan ta lallasa Zenit 2-1 a shekaran jiya. Ta uku itace kungiyar RB Leipzig wadda ta cire Manchester United a gasar bayan ta lallasa ta 3-2 kuma kasance ta biyu a Group H da maki 12. Ta karshe itace Borussia Monchengladbach wadda tasha kashi 2-1 a hannun kungiyar Real Madrid a daren jiya, amma duk da haka ta cancanci buga wasannin karshe na gasar sakamakon ta kasance ta biyu a Group B na gasar da maki 8.
Midtjylland 1-1 Liverpool, Ajax 0-1 Atalanta: Salah yaci kwallon Liverpool mafi sauri a gasar zakarun nahiyar turai yayin da Ajax ta fita a gasar

Midtjylland 1-1 Liverpool, Ajax 0-1 Atalanta: Salah yaci kwallon Liverpool mafi sauri a gasar zakarun nahiyar turai yayin da Ajax ta fita a gasar

Wasanni
Kungiyar Liverpool wadda ta kasance a saman D na gasar zakarun nahiyar turai ta raba maki da kungiyar Midtjylland bayan sun tashi wasa 1-1, kuma kiris ya rage Liverpool ta lashe gabadaya makin wasa amma VAR ta soke kwallon da Takumi yaci sakamakom ta tabi hannun Sadio Mane. Mohammed Salan ne ya ciwa Liverpool kwallo guda cikin dakikai 55 da fara wasan, wadda ta kasance kwallo mafi sauri da Liverpool taci a tarihinta na gasar, kuma kwallon tasa yanzu ya Salah ne dan wasan daya fi ciwa Liverpool kwallaye masu yawa a gasar bayan yaci 22 sannan ya wuce Steven Gerard da kwallo guda. Tauraron dan wasan Atalanta, Muriel ya taimakawa kungiyar tashi ta cancanci buga wasannin karshe na gasar zakarun nahiyar turai bayan ta cire Ajax a gasar,  sakamakon lallasa ta 1-0 data yi.
Sakamakon wasannin Champions League, yayin da Real Madrid da Atletico Madrid suka cancanci buga wasannin karshe na gasar

Sakamakon wasannin Champions League, yayin da Real Madrid da Atletico Madrid suka cancanci buga wasannin karshe na gasar

Wasanni
Manchester City tayi nasarar kasancewa a saman Group C na gasar zakarun nahiyar turai da maki 16 bayan ta lallasa Marseille 3-0 ta hannun Ferran Torres, Aguero da kuma Sterling, yayin da itama Porto ta lallasa Olympaicos 2-0 a Greece kuma ta kasance a ta biyu a Group C din da maki 13. Real Madrid tayi nasarar lallasa Monchengladbach 2-0 ta hannun Benzema kuma ta kasance a saman Group B na gasar zakarun nahiyar turai da maki goma. A karshe dai sakamakon wasa yasa yanzu Madrid da Monchengladbach duk sun cancanci buga wasannin karshe na gasar. Kungiyar Inter Milan kuwa ta fita a gasar bayan sun tashi wasa 0-0 da Shanktar Donetsk wadda ita yanzu ta fada gasar Europa League. Kungiyar Bayern Munich ta kasance a saman Group A na gasar ta zakarun nahiyar turai da maki 16 bayan ta lallasa Lok...