fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Tag: Chibok

Hotuna: A karin farko daliban Chibok sun rubuta jarabawar WAEC bayan shekaru 6

Hotuna: A karin farko daliban Chibok sun rubuta jarabawar WAEC bayan shekaru 6

Uncategorized
Daliban makarantun karamar hukumar Chibok dake jihar Borno a karin farko sun rubuta jarabawar WAEC bayan shekaru 6 basu samu damar rubuta jarabawar ba saboda matsalar tsaro.   A shekarar 2014 ne Boko Haram suka sace dalibau mata 200 daga makarantar mata ta Chibok wanda hakan ya dauki hankalin Duniya, saidai a yanzu makarantar matan ta Chibok ta zama ta maza da mata.   Rundunar sojojin Najeriya ta 7 ta bayyana cewa ana rubuta jarabawar a karin farko cikin shekaru 7 tare da bada tsaron da suke.   Sannan ta bayyana cewa shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai na bayar da gudummawa da sojoji wajan karantar da dalibai a karamar hukumar.