
Ji halin ban tausai da marasa lafiya suka shiga yayin da Likitocin Najeriya suka fara yajin aiki, Gwamnati ta yi barazanar daukar mataki
Kungiyar Likitocin Najeriya ta NARD ta shiga yajin aiki duk da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin tarayya.
Hakan yasa asibitoci a jihohi da dama suka daina karbar marasa lafiya idan ba wanda ke cikin halin bukatar kulawar gaggawa ba.
Rahoton punchng ya bayyana cewa, mutane da yawa masara lafiyane suka ziyarci asibitoci yayin da aka fara yajin aikin amma babu Likitocin da zasu kula dasu. An rika ce musu su koma gida.
A Asibitin Kano, Rahoton ya Bayyana cewa, mutane sun rika dauke danginsu daga Asibitin Gwamnati saboda yajin aikin.
A matarnin gwamnati kan wannan lamarin, Ministan kwadago, Chris Ngige ya bayyana cewa, bai kamata ba abinda Likitocin suka yi. Yace ana maganar rayuwar jama'a ne, kuma zasu basu nan da zuwa karshe mako, idan...