
Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya Philippe Coutinho
An shawarci kungiyar Chelsea cewa ba sai sun siya Coutinho ba a wannan kakar wasan saboda suna da dan wasan dake buga masu lamba 10. Daya daga cikin masu sharhi na ESPN Don Hutchison yace Chelsea zasu rasa Christian Pulisic in har suka siya dan wasan Brazil din.
Chelsea suna samun nasara wurin siyan dan wasan Brazil din yayin da Bayern Munich suka fasa siyan shi bayan sun aro shi daga kungiyar Barcelona. Barcelona suna kokarin siyar da dan wasan domin su samar ma Neymar da Lautaro Martinez matsugunni a kungiyar duk da cewa bai zama lallai su siya gabadaya yan wasan ba.
Hutchison yana gargadin Chelsea gami da siyan Philippe coutinho da suke so suyi saboda zasu rasa Christian Pulisic.
Dan wasan amurikan Pulisic ya shiga kungiyar Chelsea ne a kakar wasan bara a farashin e...