
Gwamnatin tarayya na iya sake bude makarantu nan ba da jimawa ba, – A cewar karamin Ministan Ilimi Nwajiuba,
Karamin Ministan Ilimi, Mista Chukwuemeka Nwajiuba, ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara duba yiwuwar sake bude makarantun a fadin kasar.
Nwajiuba ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawabi a gaban kwamitin yaki da cutar Korona a ranar Litinin a Abuja.
Kodayake ya ce har yanzu ba a sanya ranar da za a koma makarantun ba.
Sai dai Ministan ya yi kira ga daliban da ke zanga-zangar da su “yi hakuri.
A cewarsa, Har yanzu gwamnati tana cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki don dubu yiwuwar sake bude makarantun.
Idan zaku tuna, an rufe makarantun sakandire dana gaba da sakandire a sakamakon barkewar cutar coronavirus tun a ranar 9 ga watan Maris na wannnan shekara.