fbpx
Thursday, June 8
Shadow

Tag: Cin Amana

Bidiyo: Yanda miji ya tattaro abokansa suka lakawa matarsa da kwartonta duka bayan kamasu turmi da Tabarya

Bidiyo: Yanda miji ya tattaro abokansa suka lakawa matarsa da kwartonta duka bayan kamasu turmi da Tabarya

Siyasa
Wani magidanci da ya kamata matarsa da kwartonta Turmi da tabarya a Otal ya tattaro abokansa suka lakada mata duka ita da kwarton.   Lamarin ya farune a kasar Zimbabwe inda aka ji wasu a cikin Bidiyon na fadar cewa idan da bata son mijin nata ai da rabuwa ta yi dashi maimakon ta rika cin amanarsa.   Daga baya dai mijin ya gane Kwarton. https://youtu.be/4t3rOW1o-jc
Wani Mutum Ya Gurfana A Gaban Kotu Akan Zargin Yaudaran Miliyan N3.9 a Abuja

Wani Mutum Ya Gurfana A Gaban Kotu Akan Zargin Yaudaran Miliyan N3.9 a Abuja

Kasuwanci
Wani dan kasuwa mai suna, Mustapha Umar, ya bayyana a ranar Talata a Kotun Majistare ta Life Camp, Abuja, bisa zargin sa da cin amanar wani mutum miliyan N3.9. Umar, wanda bai amsa laifin ba ana tuhumar shi da aikata laifuka biyu na cin amana da yaudara. Lauyan mai gabatar da kara, Peter Ejike, yayin da yake gabatar da karar ya shaida wa kotun cewa wanda ya shigar da karar, Muhammed Abdullahi na Nasarawa Avenue, War College Quarters, Gwarimpa, Abuja, ya ba da rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Life Camp a ranar 1 ga Yuni. Ejike ya yi zargin cewa wanda ake kara a ranar 19 ga Maris, ya sayi daskararren kaji wanda yawansu ya kai miliyan N4.3 daga hannun mai kara. "Ya biya wasu kudade kuma cikin rashin gaskiya ya ki biyan miliyan N3.9" in ji mai gabatar da kara. Ya ...
Bidiyon yanda aka kama wani Fasto yana lalata da matar wani: Yayi ta rokon kada a fallasashi

Bidiyon yanda aka kama wani Fasto yana lalata da matar wani: Yayi ta rokon kada a fallasashi

Uncategorized
Wannan bidiyon ya nuna yanda aka kama wani fasto dake lalata da matar wani a daki. Bidiyon dai ya nuna Faston ba kaya a jikinshi inda ya duka kasa yake ta rokon kada a fallashi.   Babu dai cikakken rahoton inda abin ya faru amma bisa yanda suke magana, masu sharhi da dama sun bayyana cewa a jihar Ondo ne. Faston ya rika fadar cewa baya son Bisiyon ya yadu.
Mata ta lalata al’aurar Mijinta bisa zargin cin Amana

Mata ta lalata al’aurar Mijinta bisa zargin cin Amana

Auratayya
Hukumar Civil Defence ta jihar Osun ta bayyana cewa ta samu korafi akan wata mata data lalatawa mijinta Al'aura bisa zargin da take masa yana cin amanarta.   Me magana da ywun Hukukmar Civil Defence na jihar, Daniel Adigun ne ya bayyana haka inda yace wata mata, Omolara Seriki ce ta kai musu korafin mijinta cewa baya kula da 'ya'yansu hakanan baya bata hakkinta a matsayin matarsa.   Saidai da aka tuhumi mijin sai ya bayyana cewa shekarar su 6 da aure amma matarnan baya hin dadin zama da ita duk da suna da yara 2.   Yace ya gaji da cin zarafin da take masa shiyasa ya bar mata gidan ya koma gefensa can da zama. Wata rana wata tazo kaimai abinci sai ruwan sama ya fara, dan hakane ta tsaya ta fake. Yace can kawai sai yaji ana kwankwasa kofa, yana budewa ...
Yanda wannan magidancin ya daure matarshi, ya mata aski, ya caccaka mata wuka akai, Ido da ciki, sannan shima ya kashe kanshi saboda zargin cin ama

Yanda wannan magidancin ya daure matarshi, ya mata aski, ya caccaka mata wuka akai, Ido da ciki, sannan shima ya kashe kanshi saboda zargin cin ama

Auratayya
Wani magidanci dake zaune da matarshi a Victoria Park Estate dake Legas, me suna Femi ya kashe matarshi ta hanyar caccaka mata wuka sannan kuma ya kashe kanshi.   Ma'auratan wanda makwautansu sukace basu san wani lamari akan su sosai ba sosai saboda makonni 3 kenan da suka koma da zama rukunin gidajen an gansu suna atisaye tare a Ranar Asabar din data gabata, 20 ga watan Yuni, kamin faruwar lamarin, ranar Lahadi, 21 ga watan Yuni.   Ranar Lahadi mazauna rikunin gidajen na Victoria sun tashi da tashin hankali.   Wani da ya bayyanawa majiyarmu ta LIB yanda lamarin ya faru, yace mijin na shakku akan dansa na 2 wanda yana rika yiwa matarshi tambaya akanshi.   Yace wajan tsakiyar Rana a jiya,Lahadi, makwabtan mamatan sun rika jin karar sautin rediyo s...
Bayan shekaru 7, Wannan bawan Allahn ya gano cewa bashine uban dan da yake raino ba:Abinda ya faru daga baya ya daga masa hankali fiye da wannan

Bayan shekaru 7, Wannan bawan Allahn ya gano cewa bashine uban dan da yake raino ba:Abinda ya faru daga baya ya daga masa hankali fiye da wannan

Auratayya
Lamarin cin Amana tsakanin Ma'aurata abune da yaki ci yaki cinyewa wanda malamai na bangaren kowane addini ke Allah wadai dashi.   Babu wanda zai so Masoyinshi ya ci amanarsa dan irin hakan akwai kuna sosai da bata Misaltuwa wanda wasu masu raunin zuciyar kodai su kashe masoyin nasu ko kuma su kashe kansu.   Akwai wani da muke hira dashi da ya taba fadar cewa shifa bazai taba yin bincike akan 'ya'yansa ba wai ko nashine ko ba nashi bane, koda kuwa ba nashi dinne ba bazai so ya sani ba. Ya kara da cewa idan ma har ta kai ga gwajin kuma aka gano cewa ba dan nashi bane, zai ci gaba da rikeshi kuma zai ci gaba da zama da matarsa.   Irin hakane ta faru da wani mutum, kamar yanda ma'abocin Twitter, Jake Okechukwu Effoduh ya labarta.   Yace wani abokins...
Matar Aure ta mutu a dakin Limami

Matar Aure ta mutu a dakin Limami

Uncategorized
Wani limamin Coci a Lusaka, kasar Zambia me suna Abel Mwelwa na fuskantar dakatarwa bayan da aka samu masoyiyarshi,matar aure ta mutu a dakinshi bayan sun gama lalata.   Matar wadda hadimar cocin Katolika ce ta wa mijinta karyar cewa zata je jana'aiza amma sai ta kare a gidan limamin.   Babban limamin cocin,Alick Banda ya aikawa Abel sakon cewa an dakatar dashi har sai mama ta gani.   Wasu abokan aikin mamaciyar sun tabbatar da cewa, ta mutu a dakin limamin wanda sune ma ya kira suka dauke gawarta.
Malamar jinya ta sacewa me cutar Coronavirus/COVID-19 da ya mutu kudinsa

Malamar jinya ta sacewa me cutar Coronavirus/COVID-19 da ya mutu kudinsa

Uncategorized
Wata malamar jinya a Birnin New York na kasar Amurka me suna Danielle Conti 'yar kimanin shekaru 43 na fuskantar tuhumar sacewa wani majinyaci Katin siyayyarsa har guda 2.   Hukumar 'yansandan Birnin na New York ne suka bayyana haka, kamar yanda CNN ta ruwaito.   Lamarin ya farune a Asibitin State Island inda aka kwantar da Anthony Catapano me shekaru 70 a ranar 4 ga watan Afrilu, kamar yanda diyarsa, Tara Catapano ta shaidawa CNN.   Tace lokacin da akawa mahaifin nata satar hankalinsa na jikinsa amma ya rasu ranar 12 ga watan Aprilun sanadin cutar.   Tace itace ke kula da mahaifinta tun bayan rasuwar mahaifiyarta, kawai sai ta ji an caje ta kudi yayin da yake kwance a Asibiti Magashiyan. Haka ne yasa ta je aka mata bincike sai gashi ashe Dan...
An gurfanar da Mijin daya kwararawa matarshi ruwan zafi saboda zargin cin Amana a kotu

An gurfanar da Mijin daya kwararawa matarshi ruwan zafi saboda zargin cin Amana a kotu

Auratayya
Hukumar 'yansandan jihar Osun ta gurfanar da Akinde Adeniyi gaban kotun Majistre dake garin Ille-Ife ida ake zarginshi da zubawa matarshi ruwan zafi saboda zargin tana cin amanarsa.   Mijin dai ya zubawa matar tasa tafasashshen ruwan barkono ne tana kwance wanda hakan ya sa mata jiwuka a jiki, kamar yanda mai kara Inspectir Ona Glory ta bayyanawa kotu.   Ta kara da cewa ya yi wannan aika-aika ne a Ranar 14 ga watan Afrilun data gabata inda hakan ya jiwa matarsa Alani Deborah ciwo.   Saidai mijin ya musanta laifin da ake zarginsa dashi kuma lauyansa ya bukaci a bayar da belinsa.   Mai shari'a Joseph Owolawi ya bayyana cewa, ya bayar da belin mijin kan Naira Dubu 100 da kuma wanda zai tsaya masa me yawan irin wannan kudin. Ya kuma daga shari'ar...