
An kama Faston Najeriya da ya baiwa ma’aikatan gwamnati cin hanci a kasar Zimbabwe
Wani fasto a kasar Zimbabwe, Nixon Chibuzor Ohizu wanda dan Asalin Najeriya ne ya shiga hannun hukumomin kasar Zimbabwe inda aka kamashi ya baiwa wasu jami'an hukumar kula da jiragen kasa ta kasa 2 cin hancin Dala Dubu 2.
Dan shekaru 46 ya baiwa jami'an hukumar ta NRZ cin hancinne dan su yadda su soke wata kwangilar karya da ya shiga da hukumar tasu. Hutudole ya samo muku cewa sun amince masa cewa zasu soke kwangilar inda suka nemi ya je ya kawo kudin.
Saidai bai san ashe tarko ne suka dana masa ba, bayan da ya dauko kudin 'yan Dala 100 sai aka kamashi. An dai daureshi saidai daga baya an bada belinsa akan dala Dubu 10 inda kuma aka kwace fasfonsa.