fbpx
Monday, December 5
Shadow

Tag: Civil Defence

Allah ya kiyaye Tsautsai: Bidiyon ‘yansanda 3 na kokarin kwacewa jami’in Civil Defence Bindiga amma sun kasa

Allah ya kiyaye Tsautsai: Bidiyon ‘yansanda 3 na kokarin kwacewa jami’in Civil Defence Bindiga amma sun kasa

Tsaro
Wannan Bidiyon ya dauki hankula da dama saboda yanda aka ga wasu 'yansanda 3 na kokarin kwacewa jami'in Civil Defence bindiga.   Saidai sun kasa inda ake ta kici-kici. Babu dai cikakken bayanin inda lamarin ya farubko kuma dalilin faruwarsa.   Mutane daban-daban na ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akan Lamarin.   Kalli Bidiyon a kasa:    
Masu garkuwa da mutane sun kashe jami’in Civil Defence a Kaduna

Masu garkuwa da mutane sun kashe jami’in Civil Defence a Kaduna

Uncategorized
Masu garkuwa da Mutane dan neman kudin fansa sun kashe wani jami'in civib Defence da suka yi garkuwa dashi, Mr. Bulus Sanda.   Masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa dashine a gidansa dake Marabar Rido dake Kaduna, kamar yanda hukumar ta bayyana. A sanarwar da NSCDC ta fitar ta bakin shugabanta na Kaduna, Babangida Abdullahi Dutsin Man ta mikawa iyalan mamacin sakon ta'aziyya tare kuma da kira ga mutane su rika bada hadin kainwajan kai rahoton duk wani lamari da basu gane ba.   Hukumar ta bayyana marigayin a matsayin haziki da ke nuna kwarewa a aikinsa.
Shugaba Buhari ya karawa shugaban Civil Defence shekaru 5

Shugaba Buhari ya karawa shugaban Civil Defence shekaru 5

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tsawaita mukamin shugaban Civil Defence, Abdullahi Gana Muhammadu da shekaru 5.   Abdullahi Gana ne da kansa ya bayyana haka a yayin da yake bikin cika shekaru 5 akan mukamin. Ya bayyana cewa yana fatan wannan tsawaitawar mukami da shugaba Buhari ya masa ta amfani ma'aikatar ta Civil Defence. Me magana da yawunsa, Okeh Emmanuel ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda yace shugaba Buhari ta hannun ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya kara mukamin nashi.   Yace yana fatan za'a hada hannu dan ciyar da hukumar gaba.