
An samu karin mutum 779 wanda suka kamu da cutar coronavirus/covid-19 a Najeriya, jimulla 24,077
Kamar yadda cibiyar yaki da cututtuka ta fitar da sanarwar samun karin mutum 779 wanda ya kai adadin mutum 24,077 na wanda suka harbu da cutar corona a fadin kasar.
Cibiyar ta fitar da rahoton samun karin ne inda ta wallafa a shafinta dake kafar sadarwa na tuwita a ranar Asabar.
Hukumar ta zayyana jahohi 22 da aka samu rahoton bullar cutar a kasar wadanada ya hada da jahohin :
Lagos-285 Rivers-68 FCT-60 Edo-60 Enugu-56 Delta-47 Ebonyi-42 Oyo-41 Kaduna-19 Ogun-18 Ondo-16 Imo-12 Sokoto-11 Borno-9 Nasarawa-8 Abia-5 Gombe-5 Kebbi-5 Kano-4 Yobe-3 Ekiti-3 Osun-2.
https://twitter.com/NCDCgov/status/1277009509416927238?s=20
Baya ga haka cibiyar ta bayyana sallamar adadin mutum 8,625 tare da samun mutuwar mutum 558.